Amana ta wadanda na taimaka suka ci - Rochas

Amana ta wadanda na taimaka suka ci - Rochas

- Siyasar Imo tana ta sauya salo tun bayan firamaren APC

- AA ta tsayar da nata dan takarar wanda gwamna Rochas ke so

- Buhari yace ba sai anyi sak a jihar ba

Amana ta wadanda na taimaka suka ci - Rochas

Amana ta wadanda na taimaka suka ci - Rochas
Source: UGC

A kokarin shugaba Buhari na samar wa da magoya bayansa turba koda ba jam'iyya daya suka fito ba, da yaje jihar Imo sai yace kowa ya zabi abinda yake so, ba sai anyi sak ba.

Gwamna Rochas dai ya tayar da nasa dan takarar ne a jam'iyyar AA, bayan APC ta hana ma nasa takara, wadda APC a hannun Adams Oshiomhole tayi wa gwamnoni da dama.

GA WANNAN: Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC

A cewar Rochas dai, an ci amanarsa, musamman ganin yadda ya bautawa jam'iyya ya kuma kyautata wa wadanda yake ganin a karkashinsa suke.

Gwaman yace musamman Adams Oshiomhole, da ma Rotimi Amaechi, sune ummul aba-isin wahalarsa a siyasance a kwanakin nan, mutane da ya dauka shaqiqansa ne.

Su dai, sun hada kai da Bola Ahmad Tinubu sun ki yarda ya tsayar da surukinsa a matsayin gwamnan jiharsa ta Imo, lamari da janyo har Buhari ya sanya baki.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel