Zabe: Tsofin Janar 71 sun goyi bayan takarar shugaba Buhari

Zabe: Tsofin Janar 71 sun goyi bayan takarar shugaba Buhari

Tsofin janar a rundunar soji ta sama, kasa, da ruwa sun bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari domin sake zama shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

A yau, Litinin, ne tsofin janar din sojin su ka shaida wa duniya goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari a zaben da za a yi ranar 16 ga watan Fabarairu da mu ke ciki.

Tsofin janara-janar din sun hada da ma su mukamin manjo janar 13, Air Vice Marshal (AVM) 8, Rear Admiral 2, birgediya janar 12, Air Commodore 9, Commodore 8 da kuma wasu tsofin shugabannin rundunar soji 17.

Tsohon gwamnan jihar Legas a mulki soji, Birgeiya janar Buba Marwa (mai ritaya) ne ya jagoranci tsofin janar-janar din yayin da su ke bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari a yau.

Daga cikin tawagar tsofin janar-janar din akwai Navy Capt Caleb Olubolade, tsohon ministan harkokin 'yan sanda lokacin mulkin Jonathan da kuma tsohon shugaban rundunar sojojin ruwa ta kasa, Admiral Jubril Ayinla.

Zabe: Tsofin Janar 52 sun goyi bayan takarar shugaba Buhari

Buhari
Source: Facebook

Goyon bayan tsofin sojojin na zuwa ne bayan shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya ce manyan tsofin janar na soji da ke kasar nan na kulle-kullen kawo karshen gwamnatin shugaba Buhari ta kowacce hanya.

DUBA WANNAN: Buhari ya fadi rukunin 'yan Najeriya da ke goyon bayan sa a yaki da cin hanci

Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin gabatar da tutar takara ga gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, dan takarar gwamna a jam'iyyar APC, a filin taro na Malam Aminu Kano da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Ya bayyana cewar tspfin janar din sojin na son ganin bayan gwamnatin shugaba Buhari ne saboda irin aiyukan da Buhari ke yi ga jama'ar Najeriya ya saba wa bukatun su.

Oshiomhole ya kara da cewar sha'awar shugaba Buhari na son kyautata wa talaka ne babban dalilin da yasa tun a farko tsofin janar na sojin ke murde ma sa zabe tun a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel