Kamfen din Buhari: 'Yan kasuwa a Kano sun rufe shaguna don tsoron barkewar rikici

Kamfen din Buhari: 'Yan kasuwa a Kano sun rufe shaguna don tsoron barkewar rikici

A yau Alhamis, wasu 'yan kasuwa da dama a jihar Kano sun kulle shagunansu saboda isowar Shugaba Muhammadu Buhari jihar inda zai kaddamar da yakin neman zarcewarsa a kan mulki.

Wasu daga cikin 'yan kasuwan da su kayi magana da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN sun ce ya zama dole su rufe shagunansu ne saboda tsaro yayin da wasu kuma sun rufe shagunansu ne domin su hallarci taron kaddamar da yakin neman zaben.

Usaman Bala, wani mai shaga a fitaciyyar kasuwar Kwari da ke Kano ya ce yawancin mutane sun rufe shagunansu ne domin kasuwar ba ta da nisa da wurin da za a kaddamar da yakin neman zaben kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kamfen din Buhari: 'Yan kasuwa a Kano sun rufe shaguna don tsoron barkewar rikici

Kamfen din Buhari: 'Yan kasuwa a Kano sun rufe shaguna don tsoron barkewar rikici
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

"Domin tsare kayayakin mu, yawancin mu bamu tafi kasuwa ba a yau. Wasu kuma sun bude shagunansu da safe sannan suka rufe yayin da rana tayi," inji Bala.

Kazalika, wasu masu kananan shaguna a titin asibitin kwararu na Murtala Muhammaed da kasuwar Rimi suma sun rufe shagunansu saboda kusancin ta da wurin taron.

Wani dan kasuwa mai suna Yahuza Aminu ya ce sun shiga mawuyacin hali a makon da ta gabata da wata jam'iyyar siyasa ta kaddamar da yakin neman zabenta a filin wasannin na Sani Abacha.

"Matasa dauke da makamai suna ta kwashe wayoyin salula da kudade daga hannun masu shaguna. Saboda haka kowa yana kokarin kiyaye abinda ya faru a baya shi yasa aka rufe shaguna," a cewar Aminu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel