Dakatar da Cif Joji: Matasan Kano sun ja kunnen Shugaba Buhari

Dakatar da Cif Joji: Matasan Kano sun ja kunnen Shugaba Buhari

- Wata kungiyar matasan jihar Kano sunyi kira ga shugaban kasa Buhari ya yi gaggawar mayar da Walter Onnoghen kan mukaminsa

- Kungiyar matasan ta KKV ta ce ba ayi biyaya ga kundin tsarin mulkin kasa ba wurin tsige Justice Walter Onnoghen

- KKV tayi barazanar cewa muddin Shugaba Muhammadu Buhari bai mayar da Alkalin Alkalan ba za suyi amfani da kuri'unsu su kayar da shi a zaben 2019

Matasan Kano sun bukaci Buhari ya mayar da Onnoghen kan mukaminsa

Matasan Kano sun bukaci Buhari ya mayar da Onnoghen kan mukaminsa
Source: Depositphotos

Wani hadakar matasan Jihar Kano masu dauke da katin zabe mai suna Kano Voter's Voice (KVV) sunyi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da Alkalin Alkalai, CJN Justice Walter Onnoghen zuwa mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.

A yayin da ya ke hira da manema labarai a madadin kungiyar a ranar Laraba, Shugaban Kannywood door-to-door Initiative, Malam Mika'il Isa Bn Hassan ya ce fannin shari'a sashi ne mai cin gashin kanta a gwamnati.

DUBA WANNAN: Dakatar da Onnoghen: Matasa sun yiwa shugaban kungiyar lauyoyi duka a jihar Ribas

Ya kara da cewa doka ya bayyana karara cewa dakatar da Mr Onnoghen ya sabawa tanadin da kundin tsarin dokar kasa ta tanada.

"Ba ayi biyaya ga doka ba wurin tsige Alkalin Alkalai saboda sashi na 292 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayyana hanyar da za a bi idan ana son a dakatar ko tsige Alkalin Alkalai na kasa.

"Batun dakatar da Alkalin Alkalan na kasa yana bata wa Najeriya da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje suna a idanun kasashen duniya," inji shi.

Ya ce muddin shugaban kasa bai mayar da Onnoghen kan mukaminsa ba, hadakar matasar ba su da wata zabi illa suyi amfani da katin zabensu suyi waje da gwamnatin idan babban zabe ya zo ba.

Ya ce demokradiyyar Najeriya har yanzu sabuwa ce kuma hanyar da za a bi domin tarairayarta itace biyaya ga doka da oda wurin zartar da hukuncin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel