Shekaru har 25 aka yanke wa matar da tayi sata kacal a Osun

Shekaru har 25 aka yanke wa matar da tayi sata kacal a Osun

- An yankewa wata mata hukuncin shekaru 25 a gidan yari

- An kama ta laifin satar kudi har Naira miliyan 4.5

- Ta sace kudin da aka bata ajiya kuma ta saka wa ofishin wuta

Shekaru har 25 aka yanke wa matar da tayi sata kacal a Osun
Shekaru har 25 aka yanke wa matar da tayi sata kacal a Osun
Asali: UGC

Mai Shari'a Yinka Aderibigbe ta babbar kotun Osogbo jihar Osun a ranar laraba ta yankewa wata mata mai shekaru 38, Toyin Raheem hukuncin shekaru 25 a gidan yari akan satar Naira miliyan 4.5.

Wanda ya gurfanar da ita, Mr Abiodun Badiora ya sanar da kotu cewa matar ta aikata laifin ne a 1 ga watan Yuni, 2018 da gurin karfe 8 na safe.

Yayi bayanin cewa wacce aka dauren ma'aikaciyar wani ofishin MTN ne wanda wani kamfani mai suna Wolid Investment Limited Osogbo ya mallaka.

Badiora yace matar ta sace Naira miliyan 4,5 wanda aka bata ajiya kuma tayi yunkurin cinnawa ofishin wuta.

GA WANNAN: Tsagerun Niger Delta sunce a shirye suke da su fuskaci duk wanda ya shirya yin magudi a zaben shekara 2019

Yace wacce aka yankewa hukuncin taso yaudarar mamallakin gurin kasuwancin cewa kudin sun kone a ginin kafin a kashe wutar.

Kamar yadda laifin ta suka nuna, yaci karo da sashi na 443, 390, 1 kuma abin hukuntawa a karkashin sashi na 1 sakin layi na uju na hukunce hukunce laifukan damfara na 2006 na dokokin jihar Osun.

Lauyan wanda ake kara, Mr Abdulfatai Abdulsalam ya roki kotun da tayi adalci da jin kai a gurin hukunta ta.

Yace wacce aka yankewa hukuncin karo na farko kenan da tayi laifi Kuma ta koyi darasi.

Mai shari'a Aderibigbe ta yanke mata shekaru 25 a gidan kaso.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel