Babban bankin Najeriya na duba yadda zai ajje kudin ruwa a bana
- Babban bankin Najeriya CBN bai canja tsarin bawa bankuna bashi ba
- Bankin yayi hakan ne dan kokarin dakatar da harkokin kudi daga tashin gwauran zabi
- Anbar tsarin a yanda yake na kaso 14%

Asali: UGC
A ranar Talata ne babban bankin Najeriya ya bar tsarin bawa bankuna kudin ruwa da yadda zasu amshe shi, a yanda yake ba tare da canji akan hakan ba.
Gwamnan bankin Godwin Emefiele ya bayyanawa manema labarai cewa bayan zaman da MPC sukayi a Abuja sunbar tsarin a yanda yake akan kaso 14%.
Mr Emefiele tace sunbar tsarin akan hakan ne dan kokarin dakatar da harkokin kudi daga tashin gwauran zabi.
GA WANNAN: Tsagerun Niger Delta sunce a shirye suke da su fuskaci duk wanda ya shirya yin magudi a zaben shekara 2019
Bankin yana tafiya akan wannan tsari tsayin watanni 30 da suka shude tun daga watan Yuli shekara ta 2016.
Sannan ya janyo hankalin gwamnati akan hatsarin dake cikin kari akan matakin rance wanda yake kokarin komawa gidan jiya.
Shi dai kudin ruwa, watau interest rate, shine ribar da bankunan ke amsa muddin mutum ko ofishi ko wani bankin ya amshi kudi don yin kasuwanci.
Kudin ruwa a 14% na nufin in ka ari N1m. a shekara zaka biya 1.14m ko ka dora N140,000 a kan miliyan dayar.
Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa
Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng