Obasanjo da gumin mahaifina ya ke ci amma ko tunawa da shi ba ya yi - Jami'u

Obasanjo da gumin mahaifina ya ke ci amma ko tunawa da shi ba ya yi - Jami'u

Jami'u Abiola, babban dan marigayi Cif MKO Abiola, ya caccaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a kan "cin moriyar ganga da yasar da kwaurenta" ta hanyar kin tuna wa da mahaifin su da ya mutu a fafutikar kafa dimokradiyya a Najeriya.

Marigayi Abiola ne ya lashe zaben ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 da tsohoon shugaban kasa a mulkin soji, Ibrahim Babangida (IBB), ya rushe. Saboda abin da ya faru ga marigayi Abiola ne aka bawa Obasanjo takarar shugaban kasa a 1999 bayan dawowar dimokradiyya domin share wa 'yan kabilar Yoruba hawaye.

Dan marigayin na wadannan kalamai ne jiya, Lahadi, a wurin wani taro da aka yi a Abuja a kan shaidar irin cigaban da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo tun bayan fara mulkin ta a 2015.

Kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar, ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ne ya shirya taron domin bawa wadanda suka amfana da aiyukan gwamnatin Buhari damar tofa albarkacin bakinsu.

Obasanjo da gumin mahaifina ya ke ci amma ko tunawa da shi ba ya yi - Jami'u
Obasanjo
Asali: Getty Images

Jamiu, daya daga cikin wadan da su ka yi magana a wurin taron, ya yi waiwaye a kan yadda aka hana mahaifinsu hakkinsa kuma aka kashe shi, lamarin da ya ce ya saka su cikin matsanancin hali.

Jamiu ya ce Obasanjo ya fi kowa cin moriyar irin gwagwarmayar siyasa da mahaifinsu, Abiola, da mahaifiyar su, Kudirat Abiola, su ka yi.

DUBA WANNAN: Irin halayen Abacha gare ka, Obasanjo ya sake rubuta buddadiya ga Buhari

Ya ce, duk da kasancewar Obasanjo da mahaifinsa sun fito daga jiha guda, tsohon shugaban kasar ya yi burus da duk kokarin na kusa da shi na karrama marigayi Abiola da tuna wa da irin gudunmawar da ya bawa dimokradiyya a Najeriya.

"Shugaba Buhari ba dan kabilar Yoruba ba ne, amma shine ya share mana hawaye ta hanyar karrama mahaifin mu tare da tuna wa da irin gudunmawar da ya bayar a bangaren dorewar siyasa a Najeriya," a cewar Jamiu.

Kazalika ya yaba wa kokarin gwamnatin Buhari na inganta rayuwar jama'a da kawo canji a yadda ake tafiyar da gwamnati da mulki a Njeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel