Garkuwa da Mutane: Mazauna jihar Katsina sun fara komawa kasar Nijar

Garkuwa da Mutane: Mazauna jihar Katsina sun fara komawa kasar Nijar

Mun samu cewa, da yawa daga cikin al'ummar Najeriya mazauna jihar Katsina, sun fara gudun tsira na sauya sheka zuwa makociyar kasa ta Nijar a sakamakon annobar garkuwa da mutane da ta yi kamari da kuma matsin lamba ta 'yan baranda.

Binciken manema labarai na jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, da yawan mutanen jihar Katsina sun fara tattara iyalan su wajen sauya sheka zuwa kasar Nijar tare da mallakar fulotai da gina muhallai musamman a babban birnin kasar Nijar na Maradi da kuma Dan Issa.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, tuni wasu daga cikin al'ummar jihar Katsina sun fara mallakar takardun lasisi domin samun 'yancin zama a kasar ta Nijar da ke yankin Yammacin Afirka.

Garkuwa da Mutane: Mazauna jihar Katsina sun fara komawa kasar Nijar
Garkuwa da Mutane: Mazauna jihar Katsina sun fara komawa kasar Nijar
Asali: UGC

Lamarin ta'addanci na masu garkuwa da mutane yayi kamarin gaske cikin 'yan kwanakin nan a jihar Katsina, inda da yawan mazauna jihar ke afkawa cikin tarkon masu ta'ada tare da biyan kudaden fansa masu tarin yawa wajen ceto masoyan su.

A watan Dasumba na shekarar da ta gabata ne gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi korafin yadda ta'addancin masu garkuwa da mutane ke ciwa jihar sa tuwo a kwarya tare muzgunawa zaman lafiyar al'ummar sa.

Kazalika jihar Zamfara da ke makotaka da Katsina, ta yi kaurin suna wajen fuskantar mummunar ta'ada ta masu garkuwa da mutane tsawon shekaru kadan da suka gabata da tasirin hakan ya salwantar da rayukan daruruwan mutane musamman a shekarar 2018 da ta gabata.

Mafi akasarin attajirai da masu hannu da shuni na al'ummar jihar Katsina da ke ci gaba da neman tserewa halaka ta hanyar sauya sheka sun fito ne daga karamar hukumar Jibia da ke daf da iyaka ta kasar Najeriya da kuma Nijar.

KARANTA KUMA: Tsoho mai shekaru 103 ya yi tsalle ta taga domin tserewa gobara

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, mazauna kauyukan Fafara, Shinfida, Tsambe da kuma Gurbi da ke karkashin karamar hukumar Jibia na gudanar da harkokin su na kasuwanci a cikin kasar su ta gado da ta kasance Najeriya kana su kwashe dare a kauyukan kasar Nijar musamman Bimma da kuma Gabi.

Duk da rashin ci gaba na zamani a kauyukan kasar Nijar, al'ummar Najeriya sun gwammace su zauna cikin su sakamakon mafificiyar kwanciyar hankali ta fuskar ingataccen tsaro kamar yadda binciken manema labarai ya tabbatar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng