Sanatoci sun yi ittifaki a kan sukar juyin mulkin da aka yi wa Gwamnatin Shehu Shagari

Sanatoci sun yi ittifaki a kan sukar juyin mulkin da aka yi wa Gwamnatin Shehu Shagari

- Sanatocin Najeriya sun kuma yin tir da juyin mulkin da aka yi wa Gwamnatin Shagari

- Janar Muhammadu Buhari ne ya kifar da mulkin Shehu Shagari a karshen shekarar 1983

- ‘Yan Majalisar kasar sun ce wannan mugun juyin mulki ne ya dawo da Najeriya baya cak

Sanatoci sun yi ittifaki a kan sukar juyin mulkin da aka yi wa Gwamnatin Shehu Shagari
Sanatoci sun ce juyin mulkin Buhari yayi wa Najeriya barna
Asali: UGC

Juyin mulkin da Janar Muhammadu Buhari yayi wa Shehu Shagari ya gamu da sabuwar suka a zaman da majalisar dattawan Najeriya su kayi kwanan nan. Sanatocin kasar sun kuma yin tir da wannan abu da ya faru a lokacin baya.

A karshen 1983 ne Manjo Janar Muhammadu Buhari yayi waje da gwamnatin Alhaji Shehu Shagari, inda ya dare kan mulkin kasar. Sanatocin kasar nan sun bayyana cewa wannan juyin mulkin ye jefa Najeriya cikin matsala.

A Ranar Alhamis din da ta wuce ne aka yi magana game da tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari wanda ya rasu kwanakin baya. ‘Yan majalisa sun ci ma matsaya cewa ya kamata ayi abin tunawa da tsohon shugaban kasar.

KU KARANTA: 'Yan Majalisa sun nemi Buhari ya karrama Marigayi Shagari

Wani Sanatan Sokoto inda Marigayin ya fito, da kuma wasu ‘yan majalisa 9 ne su ka kawo wannan batu a majalisar dattawan inda su kayi kira ga gwamnatin tarayya ta yi wani abu da zai sa a rika tunawa da Shagari bayan rasuwar sa.

Sanata Ibrahim Danbaba da ‘yan uwan sa ne su ka kawo wannan kudiri. Sanata Mao Ohuambuwa ya bayyana cewa kifar da Shagari da aka yi yayi matukar dawo da Najeriya baya ta fuskar tattalin arziki da cigaban kasa na akalla shekaru 20

Mao Ohuambuwa da wasu Sanatocin kasar sun jinjinawa Marigayi Alhaji Shehu Shagari wanda su kace mutum ne mai kaunar jama’ar Najeriya da kokarin ganin an samu zaman lafiya da kuma hadin-kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel