Kamfen: Mai dakin Atiku ta yiwa matan Kano wata muhimmiyar alkawari
- Mai dakin Atiku Abubakar, Gimbiyya Ruqayya Atiku ta dira jihar Kano domin kaddamar da yakin neman zaben Atiku
- Gimbiyya Ruqayya Atiku ya yiwa mata alkawarin bullo da wani shiri na musamman domin tallafawa mata idan Atiku ya yi nasara
- Ruqayya Atiku ta kuma shawarci mutanen jihar Kano su guyi sayar da kuri'unsu domin shine 'yancin su da zai fitar da su daga rayuwar talauci
Mai dakin dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abukabar, Gimbiyya Ruqayya Atiku ta yiwa mata alkawarin bullo da shiri na musamman domin tallafawa mata idan mijinta ya yi nasara a babban zaben shekarar 2019.

Asali: UGC
A jawabin da tayi a wurin taron kaddamar da yakin neman zaben Atiku a jihar Kano, Gimbiyya Ruqayya ta ce Najeriya ta fuskanci koma baya a fanoni daban-daban saboda gwamnatin APC kuma ta bukaci mutanen Kano su kori APC da kuri'unsu.
DUBA WANNAN: Buhari ya fadi dalilan da yasa har yanzu ake da almajirai a Najeriya
Ta kuma sake yin kira da al'ummar Kano musamman mata da kar su yarda su sayar da katin zabensu domin shine 'yancin su.
"Kada ku sake ku bawa kowa katin zaben ku; Wannan wani sabuwar dabara ne da wasu ke amfani da ita domin hana ku zabe. Ya kamata ku gane cewa katin zaben ku shine makamin da zai fitar da ku daga kangin yunwa da talauci ya baku 'yancin kanku," inji ta.
A nata bangaren, Fanna Buba Galadima ta ce, 'yan Najeriya sun gane kuskuren da su kayi a shekarar 2015 saboda gwamnatin da suka zaba ta gaza cika musu alkawurran da ta dauka musu.
A cewarta, lokacin da-na-sani ya wuce, yanzu lokaci ne na zabe saboda haka kowa ya kasance cikin shiri da katin zabensa domin korar jam'iyyar APC daga mulki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng