Mai tsaron doka ya bige da gyangyadi, an kama ASP da wasu suna satar Jannareta
- A jihar Bauchi aka kama su da laifin
- Sun kwashi manyan Jannaretoci har biyu na miliyoyin Nairori
- Daya daga cikinsu babban dansanda ne da yayi ritaya

Asali: Twitter
An kama barayin Jannaretoci har biyu, na miliyoyin kudi a ofishin gwamnati a jihar Bauchi, su su goma suka yi kumbiya-kumbiyarsu sai da suka sace Jannaretocin masu karfin GBW 10KVA a ofishin National Public Security Communication System na jihar.

Asali: Depositphotos
Sai dai abin kunyar bai kare ba, bayan da kuma aka gano ashe daya daga cikinsu barawon zaune ne amma da kayan sarki, watau dai tsohon dansanda ne da har ya kai matsayin ASP kafin a masa ritaya.
Mai magana da yawun hukumar 'yansandan jihar PPRO Kamal Abubabakar ne ya bayyanawa manema labarai hakan a jiya alhamis a ofishin nasu.
GA WANNAN: An sake waiwayar dumbin dukiyar da Alex Badeh ya bari, sai dai an daga kafa har ayi jana'izarsa
Za dai a kaisu kotu, a kuma tuhume su tunda an kamo su su 10, kuma ana kan bincike. Fidelis Ewona dai shine shugabansu, kuma dashi da sauran 10n suna hannu.
Gwamnatin Tarayya ce dai take ta samar da manyan jannaretocin nan don a samu a gyara harkar tsaro a kasar nan, bayan da ya tabarbare, sai dai ashe muggan harda na cikin gida, masu zagon kasa da taya barayi barna.
Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa
Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng