An saka dokar ta-baci a jahar Taraba biyo bayan kazamin rikici daya barke tsakanin yan siyasa

An saka dokar ta-baci a jahar Taraba biyo bayan kazamin rikici daya barke tsakanin yan siyasa

Gwamnatin jahar Taraba ta kaddamar da dokar ta baci da za ta hana shige da fice a garin Wukari dake cikin karamar hukumar Wukari biyo bayan wani kazamin rikici daya barke a tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC da na wasu bta gari a garin.

Wannan rikici dai ya faru ne a ranar Alhamis, 17 ga watan Janairu a lokacin da dan takarar gwamnan jahar a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Alhaji Sani Danladi a garin Wukari a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa karamar hukumar Ibi.

KU KARANTA; https://hausa.legit.ng/1216234-raayin-gumi-dahiru-bauchi-jingir-bala-lau-da-yusuf-sambo-game-da-zaben-buhari-da-atiku.html

Legit.ng ta ruwaito kaakakin jam’iyyar APC na jahar Taraba, Aaron Artimas ya bayyana cewa suna kan hanyarsu ta zuwa garin Ibi da nufin gabatar da dan takararsu ga jama’a kwatsam sai aka kai musu farmaki a garin Wukari, inda aka kona musu motoci da dama.

Wannan hari da aka kai ma dan takarar gwamnan jahar Taraba a jam’iyyar APC, Sani Danladi tasa gwamnan jahar Taraba Darius Ishaku ya kaddamar da dokar ta baci a garin Wukari, wanda zai hana kowa ita daga jarfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Gwmana Ishaku ya yi kira ga jama’a dasu kasance masu yin biyayya ga doka da oda tare da rungumar zaman lafiya a dukkanin al’amuransu na yau da kullum, haka zalika yayi kira a garesu dasu baiwa jami’an tsaro goyon baya.

Shima kwamishinan Yansandan jahar Taraba, David Akinremi ya tabbatar da faruwar rikicin siyasar a lokacin da yake zantawa da manema labaru a shelkwatar rundunar Yansandan jahar Taraba dake garin Jalingo.

Daga karshe gwamnan jahar ya ja kunnen yan siyasa dasu guji yawo da yan baranda, yan jagaliyan siyasa da kuma yan daba a lokacin da suke zagayen neman kuri’un jama’a, domin a cewarsa yan daba basu da wata gudunmuwar kirki da zasu basu a zaben.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng