An sanya sunan Muhammad Ali a wani katafaren filin jirgin Amurka

An sanya sunan Muhammad Ali a wani katafaren filin jirgin Amurka

- An maida sunan filin jirgin saman Louisville Muhammad Ali International Airport

- Muhammad Ali ya zamto shaharrarre a duniya bayan ya buga wani wasa

- Ya rasu yana da shekara 74 a duniya bayan fama da jinya

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Asali: Instagram

Filin jirgin saman Louisville ya canja sunan sa zuwa Louisville Muhammad Ali international Airport.

A hukumance dai, Muhammad Ali mai lifin ne, kuma ko bayan da ya mutu kasar bata cire sunansa a masu laifin cin amanar kasa ba, bayan da ya ki ya amince yaje yakin da Amurka keyi a Vietnam a zamaninsa.

An sanya sunan Muhammad Ali a wani katafaren filin jirgin Amurka
An sanya sunan Muhammad Ali a wani katafaren filin jirgin Amurka
Asali: Facebook

Hukumar filin jirgin ta bayyana hakan ne a ranar Laraba inda tace daga yanzu filin tashi da saukar jiragen ya koma Louisville Muhammad Ali international Airport.

Muhammad Ali ya zamto shahararre a duniya bayan ya buga wani wasan dambe da George Foreman inda ya ka dashi.

A wancan lokacin Muhammad Ali yace " A yanzu baki daya duniya ta sanni amma duk wannan nasara tawa ta fara ne daga Louisville ".

GA WANNAN: Duk da tsadar man da muke ji, in ka kwatanta da sauran kasashe zaka ga mu banza muke sha

Matar marigayin Lonnie Ali tace tayi matukar farin ciki da wannan hukunci na hukumar filin tashi da saukar jiragen ta yanke.

Ali ya rasu yana da shekaru 74 a duniya bayan fama da jinya da yayi inda aka binneshi a wata makabarta dake Louisville inda dubunnan masoya ke dauke da akwatin gawar tashi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel