Zan azurta abokaina idan na zama shugaban kasa - Atiku

Zan azurta abokaina idan na zama shugaban kasa - Atiku

- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce abokansa ne ba 'yan uwa ba idan ya hau mulki

- Atiku ya bayyana cewar aboakansa na da hakkin su yi arziki a gwamnatinsa matukar ba ta hanyar cin hanci bane

- Kazalika, ya jaddada aniyar sa ta sayar da kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC) matukar ya hau mulkin Najeriya

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya ce zai azurta abokansa idan ya hau mulki.

Atiku ya bayyana haka ne a yammacin jiya, Laraba, yayin gabatar da jawabi ga taron wasu 'yan kasuwar jihar Legas a taro na musamman da aka bawa Atiku damar yin magana a kan 'hanyoyin farfado da tattalin arzikin Najeriya'.

"Ba zan azurta 'yan uwana ba sai dai abokai.

"Abokaina sun cancanta su yi arziki amma ba ta hanyar cin hanci ba," a cewar Atiku.

Zan azurta abokaina idan na zama shugaban kasa - Atiku
Atiku
Asali: Depositphotos

Bayan wannan, Atiku ya ci al washin sayar da kamfanin dillancin man fetur na kasa NNPC, matukar ya hau mulki.

"Na riga na fada tun a baya, zan sayar da NNPC," kamar yadda Atiku ya fada.

A baya Atiku ya taba sanar da cewa zai sayar da NNPC saboda rudani na tsawon shekaru da ya yi yawa a kan yadda take gudanar da lamuranta.

DUBA WANNAN: Zan canja gwamnan babban bankin kasa idan na ci zabe - Atiku

Duk da jama'a da dama sun soki wannan kudiri na Atiku, dan takarar na PDP ya ce zai aikata hakan koda zai rasa rayuwar sa.

"Na rantse ko da zasu kashe ni sai na aikata hakan," kamar yadda Atiku din ya fada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng