Azabar da suka gana min ce ta kaini yarda nayi laifin da ban yi ba - Evans
- Wani da ake tuhuma ya amsa laifin sa saboda takurar da jami'an yan sanda suka masa
- Ya sanya hannu akan takaddar da yan sanda suka bashi dan gudun karsu kashe shi
- Dana tambayi takaddun mene yan sanda sun dake ni a kai sannan suka kona min hannu da taba sigari cewar Evans

Asali: Depositphotos
A ranar Laraba ne Chukwudumeme Onwuamadike wanda akafi sani da Evans ya amsa laifin da kotun Igbosere dake jihar Legas take tuhumar sa dashi bisa ga tursasawar jami'an yan sanda.
Evans ya bayyanawa mai shari'a Adedayo Akintoye cewa ya sanya hannu a takaddun da yan sandan suka bashi ne saboda tsoron mutuwa.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin mambobin IGP da IRT sun kama shine tun a shekara ta 2017 inda suka razana shi ta hanyar kashe wadansu masu laifi kafin sukai masa hari.
Ana tuhumar Evans ne da aikata laifuka guda Biyu,kokarin yin kisan kai da kuma yin garkuwa da mutane.
GA WANNAN: Zamu dawo da martaba da kimar jiharmu, kamar yadda aka santa a da - Gwamnan Borno
Evans ya tuhumu IGP da IRT da kashe masu laifi ta hanyar dora musu jakunkunan roba sannan suka nemi ayi masa haka idan har bai basu goyan baya ba.
Ya kara da cewa wasu daga cikin takaddun da aka bashi ya sanya hannu akwai rubutu a jiki wasu kuma babu.
Evans ya kara da cewa "daya tambayi jami'an yan sandan takaddun mene sun dake shi akai sannan suka kona masa hannu da taba sigari."
Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa
Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng