Zamu dawo da martaba da kimar jiharmu, kamar yadda aka santa a da - Gwamnan Borno
- Nagartar jihar Borno zata dawo inji Gwamna Kashim Shettima
- An kaddamar da sabon shirin EGWU EKE III, wani bangare na Phython Dance
- An kaddamar da shirin ne don bayyana nasarorin da sojoji suka samu da kuma shirin gudanar da zabe mai zuwa

Asali: UGC
Gwamnan jihar Borno, Hon. Kashim Shettima ya nuna tabbacin da burin shi na dawowar nagartar jihar Borno. Gwamnan ya fadi hakan ne a ranar litinin, 14 ga watan Janairu, 2019 a Cashew Plantation, Maiduguri jihar Borno a kaddamar da fara aikin EGWU EKE III ( PHYTHON DANCE) a 7 DIVISION STEP-UP Tactical Headquarters CASHEW PLANTATION, Maiduguri.
Gwamnan wanda kakakin majalisar jihar Borno ya wakilta, Rt Hon. Abdulkarim Lawan, ya jinjinawa kokarin sojin Najeriya ta yanda suka dinga yakar yan ta'addan Boko Haram da ta'addanci ballantana a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

Asali: Facebook
A kalaman shi "Muna alfahari da sojin Najeriya kuma muna da tabbacin Nagartar jihar Borno zata dawo kuma yan jihar zasu yi farin ciki," inji shi.
Ya kara bada tabbaci tare da jaddada cewa a ba jami'an tsaro hadin kai. Mutanen jihar Borno suna da tabbacin cewa kaddamar da shirin zai kawo zaman lafiya mai dorewa a jihar.
Gwamna Shettima yayi kira ga sojin Najeriya da su cigaba da kokari tare da hada kai da sauran Jami'an tsaro da kungiyoyin taimakon kai da kai a zaben nan mai zuwa.
Kwamandan Operation Lafiya Dole Manjo Janar Benson Akinroluyo ya jinjinawa kokarin shuwagabanni da sojojin 7 Division, tare da godiya ga gwamnatin jihar akan goyon baya da suke basu tare da tabbatar musu cewa zasu cigaba da aiyukan su yanda ya dace.
GA WANNAN: Abubuwa biyu da muka sanya gaba kafin mu tafi hutun zabuka - Sanata Ahmed Lawan
A bayanin shi na farko, GOC na 7 Division kuma kwamandan sashen farko na Operation Lafiya Dole, Birgadiya janar Abdulmalik Bulama Biu yace wannan aikin tsaron cikin gida ne da aka kirkiro don duba aiyukan yan ta'adda tare da tabbatar da anyi zabe mai zuwa cikin zaman lafiya da lumana.
Ya kara da cewa mesar bazata yi kasa a guitar ba wajen hadiye duk wani Dan ta'adda ba sannan kuma mutanen jihar Borno zasu yi zabukan su cikin kwanciyar hankali.
Yayin jinjinawa gwamnatin jihar, Janar Bulama ya tabbatar da cewa an kaddamar da shirin ne don bayyana nasarorin da aka samu akan Phython dance na daya da na biyi wanda aka kaddamar a shekarar da ta gabata a yankin gabas din kasar nan.
Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa
Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng