Kotu ta kwace tikitin takarar dan majalisa daga hannun hadimin shugaba Buhari, Sha’aban
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Kano na jahar Kano ta tsige Sha’aban Ibrahim Sharada daga takarar daya tsaya ta dan majalisa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya a majalisar wakilan Najeriya, inji rahoton Daily Nigerian.
Legit.ng ta ruwaito Sharada ne hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan al’amuran watsa labaru na rediyo, kuma ya tsaya takara ne a karkashin inuwar jam’iyyar APC ta baba Buhari, sai dai ya buga da Alhaji Mukhtar Yakasai tsohon ciyaman a zaben fidda gwani.
KU KARANTA: Bikin tunawa da yan mazan jiya: Kalli yadda Buhari ya karrama Sojojin da suka mutu

Asali: UGC
Bayan an gudanar da zaben fidda gwani inda aka sanar da Sharada a matsayin wanda ya lashe zaben ne, sai abokin hamayyarsa, Mukhtar Ishaq ya kai kara gaban kotu yana neman hakkinsa, inda ya shaida ma kotu cewa shine halastaccen dan takarar APC domin shi ya lashe zaben fadda gwani akai masa murdiya.
Don haka ya bukaci kotu mai adalci data kwatar masa hakkinsa, ta hanyar bayyanashi a matsayin halastaccen dan takarar kujerar dan majalisar Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC.
Sai dai bayan sauraron duka bangarorin biyu, Alkalin kotun, mai sharia Sa’adatu Ibrahim ta bayyana cewa zaben fidda gwanin daya samar da Sharada a matsayin dan takara na cike kurakurai, don haka ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, data yi watsi da Sharada ta saka sunan Mukhtar a matsayin halastaccen dan takarar jam’iyyar APC.
Amma wani abu mai daukan hankali shine, a yayin da ake gudanar da wannan shari’a, sai gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi ma Muhktar tayin mukamin kwamishina, kuma ya amsa, inda aka nada shi kwamishinan ayyuka na musamman a makon data gabata.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng