An sake ji ma Bukola Saraki a jiharsa ta Kwara, wadansu manya da yau suka sauya sheka
- Dubbannin mutane daga Kaiama dake jihar Kwara sun bar PDP sun koma APC
- Tsohon deputy spearker na jihar ta Kwara ne ya jagoranci wannan abu
- Jam'iyar PDP tasan bazataci zaben shekara ta 2019 ba

Asali: Twitter
Dubbannin mutane daga karamar hukumar Kaiama dake jihar Kwara ne sukayi bankwana da Jam'iyar PDP suka koma APC.
Wadannan mutane sun samu jagorancin tsohon deputy speaker na jihar ta Kwara Hon.Mohammed Suka-Baba inda suka koma APC.
Sannan sun kona katin shaidar kasancewar su mambobi a jam'iyar PDP.
Da yake bayyana dalilin sa na barin jam'iyar Suka- Baba yace yabar PDP ne saboda mabiyan sa basa son jam'iyar.
"A matsayina na bafulatani na koma APC saboda mutane na APC suke so,saboda haka daga yanzu ni cikakken dzn jam'iyar APC ne."
GA WANNAN: Hodijam! Saraki ya gwale IGP guda dazunnan a filin faretin tunawa da Soji
"Sannan duk wanda yakeso yaci zabe mai zuwa to ya gaggauta komawa APC.
Da yake jawabin maraba ciyaman na jam'iyar APC a jihar Kwara Hon Bashir Bolarinwa yace "Suka-Baba yabar duhu ya dawo haske saboda APC jam'iya ce da take cika alkawari.
"PDP ta san cewa bazataci zabe mai zuwa ba saboda haka ne ta fara bullo da hanyoyin rikici.
Daga karshe yayi kira ga al'umma dasu zabi jam'iyar APC aduk wani mataki na zabe.
GA WANNAN: Yanzu kau mun tsarkaka, duk mugayen sun koma jikin Buhari - PDP ga 'yan Najeriya
Jihar Kwara dai a yanzu tana karkashin PDP ne, bayan da manyan jigoginta Gwamna da Sanata suka koma PDP, bayan jifa da kashin kaji da suka ce gwamnatin tsakiya na ta yi musu.
Kiris dai ya rage dai a baya, a gurfanar da Saraki da gwamnansa kan batun wani harin fashi a Offa a jihar, wanda hukumar 'yansanda tace akwai hannun manyan 'yan siyasar jihar a ciki, lamari da suka karyata da babban halshe.
Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa
Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng