Murnar cika shekara 20: Ali Nuhu ya jinjina wa masoyan sa

Murnar cika shekara 20: Ali Nuhu ya jinjina wa masoyan sa

Shahararren jarumin nan na wasan Hausa, da aka fi sani da ‘Sarki’ wato Ali Nuhu ya yi jinjina ga masoyan sa sannan ya gode masu bisa goyon bayansu gare shi a shekaru 20 da yayi yana gwagwarmaya a farfajiyar Kannywood.

Ali ya mika godiyar sa ga duk wadanda suka faro harkar tare a 1999 zuwa yanzu da kuma wadanda suka tallafa masa ta kowacce hanya a tsawon wannan lokaci.

Jarumin dai yayi fice a farfajiyar fina-finan Hausa matuka da wasu da dama suke ganin ba a taba dan wasa a wannan karnin tamkar sa ba.

Sakamakon gogewar sa da maida hankali ga sana’ar sa har lakabi aka yi masa da ‘Sarki’.

Cikin irin gudunmawar da ya bada a farfajiyar fina-finan Hausa, har da koyar da ‘yan wasa masu tasowa da dafa musu inda kusan dukkan su da suka jingina da shi yanzu sun zama fitattu a harkar ba a Kannywood ba har da kasa baki daya.

Murnar cika shekara 20: Ali Nuhu ya jinjina wa masoyan sa
Murnar cika shekara 20: Ali Nuhu ya jinjina wa masoyan sa
Asali: UGC

Cikin wadanda Ali Nuhu ya goya, akwai fitacciyar yar wasa. Rahama Sadau da a yanzu babu kamarta a farfajiyar Kannywood da Nollywood. Rahaman tayi ficen da har a kasashen duniya sunan ta ya karade duk a bisa goyon Ali Nuhu.

KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta saki matakan zaben 2019 (jerin matakan)

Bayan ita akwai Nafeesat Abdullahi, Zaharadden Sani, Nuhu Abdullahi, da wasu da dama.

Ya karbi kyaututtuka da dama da babu wani dan wasan Kannywood da ya taba samun irin wadanan karramawa ba a Arewacin kasar nan ba har daga kasashen Turai, Amurka da India.

Hakazalika ya fito a fina-finan Hausa sama da 1000 sannan ya fito a manyan fina-finan Turanci sama da 200 a tsawon shekaru 20 da yayi zuwa yanzu yana harkar.

Ali yana da aure da ‘Ya’ya biyu sannan shi ne ya ke bi wa Rahama Sadau a yawan mabiya a shafin Instagram.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel