Yadda Hukuncin Kotu Ya Sake Kara Damuwar da Atiku da Jam’iyyar ADC ke Ciki
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da takardar murabus din Nafiu Bala Gombe, tare da soke dukkan matakan da kwamitin David Mark ya ɗauka
- Kotun ta umarci INEC da ta amince da Gombe a matsayin kaɗai zababben mamban kwamitin gudanarwar ADC da wa'adinsa bai ƙare ba
- Rikicin ya ƙara tsananta bayan ADC ta yi barazanar ɗaukaka ƙara, yayin da 'yan takarar jam'iyyar suka kai ƙorafi ga ƙasashen duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Rikicin shugabancin jam'iyyar ADC ya sake ɗaukar sabon salo bayan hukuncin wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Kotun ta yi watsi da takardar murabus din da ake zargin tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Nafiu Bala Gombe, ya rubuta.

Source: Twitter
Hukuncin da kotun ta yi
Wannan hukunci ya ƙara dagula rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar gabanin zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisu na shekarar 2027, cewar Punch.
Matakin kotun ya zo ne bayan hukuncin da Mai Shari'a Peter Lifu ya yanke a makon da ya gabata, inda ya soke sahihancin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, ke jagoranta.
Alkalin ya kuma bayyana cewa dukkan matakan da kwamitin Mark ya ɗauka tun bayan hawansa kan mulki a ranar 29 ga Yulin 2025 ba su da inganci a gaban doka.
Wannan hukunci ya shafi dukkan abubuwan da kwamitin ya gudanar, ciki har da tsarin da ya samar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027.
Kotun ta yi wa Nafiu ƙarin bayani
A cikin takardar cikakken hukuncin kotun da wakilinmu ya samu, Mai Shari'a Lifu ya bayyana cewa dukkan matakai da shawarwarin da David Mark da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, suka ɗauka a matsayin shugabannin ADC tun ranar 29 ga Yulin 2025 ba su da wani tasiri na doka.
Sai dai alkalin ya bayyana cewa soke tsarin da ya kawo Mark kan shugabancin jam'iyyar ba yana nufin cewa Gombe ya zama shugaban ƙasa na jam'iyyar kai tsaye ba.
A cewar alkalin, akwai bambanci tsakanin soke sahihancin tsarin zaɓen shugabanni da kuma tabbatar da haƙƙin wani mutum na karɓar wani muƙami, cewar Vanguard.
Ya ce ko da Gombe ya kasance kaɗai zababben mamba a kwamitin gudanarwar ADC da bai yi murabus ba, hakan ba ya ba shi damar zama shugaban jam'iyyar kai tsaye.
Sai dai kotun ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta amince da Gombe a matsayin kaɗai zababben mamban kwamitin gudanarwar ADC wanda wa'adinsa na shekaru huɗu yake aiki.

Source: Facebook
ADC ta ƙalubalanci hukuncin kotun
A nata martanin, jam'iyyar ADC ta yi watsi da matakin kotun na bayyana takardar murabus din Gombe a matsayin takardar da aka ƙirƙira.
Jam'iyyar ta ce tana da ainihin takardar murabus din wadda take ɗauke da sa hannun Gombe, don haka ba ta yarda da hukuncin alkalin ba.
Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya shaida wa wakilinmu cewa kotun ta yi kuskure wajen yanke hukunci ba tare da yin la'akari da hujjojin da jam'iyyar ke son gabatarwa ba.
Ƙungiyar kamfen Atiku ta zargi Nafiu
A wani sabon rikici, kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC ya yi zargin cewa Gombe ya taɓa amincewa da David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar a wani taron kwamitin zartarwa na ƙasa.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya aika wa wakilinmu wani bidiyo da ake zargin Gombe ya ambaci Mark a matsayin shugaban ADC.
Ologbondiyan ya ce bidiyon ya nuna yadda Gombe ya amince da matsayin Mark a lokacin taron, duk da cewa yanzu yana ƙalubalantar shugabancinsa.
'Yan takarar ADC sun kai ƙorafi ga ƙasashe
Rikicin ya kuma janyo martani daga 'yan takarar ADC a zaɓen 2027, waɗanda suka garzaya ga ƙungiyoyin ƙasashen duniya da ofisoshin jakadancin ƙasashen waje domin neman a shiga tsakani.
Ƙungiyar 'yan takarar ADC ta ƙasa ta kai ƙorafi ga Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), ofishin jakadancin Amurka, Babban Ofishin Jakadancin Birtaniya, Tarayyar Turai (EU) da ƙungiyar ECOWAS.
'Yan takarar sun ce jinkirin fitar da cikakken kwafin hukuncin kotun na hana su amfani da haƙƙinsu na kundin tsarin mulki wajen ɗaukaka ƙara.
A cikin ƙorafin da Audu Aliyu ya sanya wa hannu a madadin ƙungiyar, sun roƙi ƙasashen da abin ya shafa da su matsa wa hukumomin Najeriya su tabbatar da bin doka da oda.
Magoya bayan ADC sun yi zanga-zanga a Abuja
A ranar Laraba, wasu mambobi da magoya bayan ADC sun gudanar da zanga-zanga a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin neman a gaggauta fitar da cikakken kwafin hukuncin.
Tsohon shugaban riƙon ƙwarya na ADC a Babban Birnin Tarayya, Yusuf Shehu Tijani, ne ya jagoranci masu zanga-zangar.
Sun buƙaci Majalisar Kula da Shari'a ta Ƙasa (NJC) ta shiga tsakani, suna zargin alkalin da ya yanke hukuncin da hana su samun takardar da za su yi amfani da ita wajen ɗaukaka ƙara.
Tijani ya bayyana hukuncin a matsayin wanda ba shi da inganci, yana mai cewa babu dalilin da zai sa kotu ta jinkirta fitar da cikakken kwafinsa.
INEC ta yi matsaya kan takarar Atiku
An ji cewa INEC ta ce ba za ta ɗauki mataki kan rikicin shugabancin ADC ba har sai ta karɓi kwafin hukuncin kotun da aka tantance.
Kwamishinan INEC, Mohammed Haruna, ya ce sashen shari’ar hukumar zai nazarci hukuncin tare da ba da shawarar matakin da ya dace.
ADC ta ƙi amincewa da hukuncin kotu, ta ɗaukaka ƙara tare da neman dakatar da aiwatar da shi har sai an yanke hukunci kan ƙarar.
Asali: Legit.ng




