Hodijam! Saraki ya gwale IGP guda dazunnan a filin faretin tunawa da Soji

Hodijam! Saraki ya gwale IGP guda dazunnan a filin faretin tunawa da Soji

- Raguwar alakar da tsakanin Saraki da shugaban yan sanda ta bayyana

- Shugaban yan sandan ya mika hannu ga Saraki amma yayi biris tare da wucewa

- Hakan bai faru tsakanin shugaban yan sandan da Dogara ba

Hodijam! Saraki ya gwale IGP guda dazunnan a filin faretin tunawa da Soji
Hodijam! Saraki ya gwale IGP guda dazunnan a filin faretin tunawa da Soji
Asali: UGC

Raguwar alakar dake tsakanin Shugaban majalisar dattawa,Bukola Saraki da Sifeta Janar na yan sanda, Ibrahim Idris, ta bayyana karara a ranar talata a Abuja, gurin bikin ranar tunawa da jami'an tsaro a inda Saraki ya ki karbar hannu da Shugaban yan sandan ya mika mishi.

Hodijam! Saraki ya gwale IGP guda dazunnan a filin faretin tunawa da Soji
Hodijam! Saraki ya gwale IGP guda dazunnan a filin faretin tunawa da Soji
Asali: UGC

Dukkanin su sunje taron da akayi a National Archade a Abuja don tunawa da kololuwar aiyukan tunawa da jami'an tsaron a shekarar 2019.

A ranar Talata ne alakar dake tsakanin shugaban majalisa Bukola Saraki da Ibrahim Idris Inspector general na yan sanda ta fito fili.

Lamarin ya afkune a yayin wani taron tunawa da sojoji da akeyi ina Saraki yaki amsar tayin gaisuwar da IGP yayi masa.

Gaba dayan su dai sun samu halartar wannan taro wanda ya gudana a National Archade a Abuja dan tunawa da sojoji a shekara ta 2019.

Shugaban yan sandan yana tsaye kusa da abin magana da aka tanada a wajen taron inda ya sarawa shugaban majalisar sannan ya mika masa hannu domin su gaisa inda Saraki ya daga kai ya kalleshi ya kauce daga wajen sa yaje ya mikawa Chief service hannu wanda suke tsaye tare da IGP din.

Amma an samu banbanci a wajen Yakubu Dogara wanda ya samu halartar taron inda ya tafi kai shaye zuwa wajen da suke ya gaisa da kowa.

GA WANNAN: An sake gwabza hadari a hanyar Legas, da yawa sun mutu

Shugaban yan sandan, wanda ke tsaye mumbari a taron, yayi sarawar girmamawa ga shugaban majalisar a shirin shi na mika mishi hannu amma a maimakon shugaban yaje gaban Idris don karbar hannun, shugaban majalisar sai ya kalle shi tare da wucewa don gaisawa da shugaban ma'aikata wanda ke tsaye tare da shugaban yan sandan.

Amma game da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara abin ba haka yake ba. Dogara ya iso taron tare da Shugaban majalisar dattawan sannan kuma yaje har kan mumbarin don karbar gaishe gaishe.

A baya dai karku manta, an zargi Saraki da daure ma 'yan fashi gindi, a wasu lokutan ma, an zarge shi da kin bayyana ainahin yawan dukiyarsa, da ma kuma sanya sunansa cikin manyan barayin kasar nan. lamari da ya sa ya bar APC.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng