Hannu da hannu nake bawa tsohon gwamna Shema cin hanci - Shaida

Hannu da hannu nake bawa tsohon gwamna Shema cin hanci - Shaida

A yau, Litinin, ne wata kotun gwamnatin tarayya ta saurari shaidar Nasir Ingawa, tsohon hadimin tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, a kan tuhumar cin hanci da ake yi masa.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da tsohon gwamna Shema a gaban kotu bisa tuhumar sa da badakalar biliyan N5.7bn kudin shirin tallafi (SURE-P) da gwamnatin tarayya ta bawa jihohi.

Yayin zaman kotun na yau ne EFCC ta gabatar da shaidar ta kuma tsohon mai taimakawa Shema a kan shirin SURE-P, Nasir Ingawa, wanda ya shaidawa kotun cewar tsohon gwamna ne da kansa ke bashi umarnin kara kudin kwangila ko fitar da kudin aiyukan bogi.

A cewar sa, "wasu aiyukan ana kara kimanin kaso 20% zuwa 30% na kudinsu bisa umarnin Shema, kuma hannu da hannu nake daukan kudin na kai masa.

Hannu da hannu nake bawa tsohon gwamna Shema cin hanci - Shaida
Ibrahim Shaida
Asali: UGC

"Wasu lokutan zai umarce ni kara kudin wasu aiyukan sannan na dauki rarar kudin na kai masa."

Ingawa, wanda lauyan hukumar EFCC, S. T. Ologunorisa (SAN), ya gabatar, ya ce wasu lokutan gwamnan kan saka shi sake biyan kudin aiyukan da aka kammala su, sannan ya umarce shi ya kai masa kudin.

DUBA WANNAN: Tirela makare da shinkafar kamfen ta murkushe mutane fiye da 20 a Ekiti

Sai dai, Elisha Kura, lauyan tsohon gwamna Shema, ya ce babu tambayar da zai yiwa Ingawa saboda bai gabatar da wata takardar shaidar cewar hakan ya faru ba.

Bayan faruwar hakan ne sai alkaliyar kotun, Jastis Hadiza Shagari, ta daga sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel