Gobara ta tafka ma dalibai mummunar barna a wata babbar makaranta dake Kaduna

Gobara ta tafka ma dalibai mummunar barna a wata babbar makaranta dake Kaduna

Wata babbar gobara ta tashi a kwalejin horas da kiwon lafiya na kimiyya da fasaha dake garin Makarfi cikin karamar hukumar Makarfi ta jahar Kaduna, kamar yadda Legit.com ta samu rahoto.

Shi dai wannan mummunan ibtila’i na gobara ya faru ne a ranar Litinin 14 ga watan Janairu a rukunin dakunan yan matan kwalejin, inda ya kona kaya tare da lalata ginin dakunan.

KU KARANTA: Tafka tafkan jiragen ruwa guda 14 sun iso Najeriya dauke da kayan abinci

Gobara ta tafka ma dalibai mummunan asara a wata babbar makaranta dake Kaduna
Kwalejin Makarfi
Asali: Facebook

Sai dai majiyoyi da dama sun tabbatar da cewar ba duka dakunan yan matan wutar ta kona ba, sakamakon dauki da sauran daliban makarantar suka kai, inda suka fiffito da kayayyakin yan matan ta hanyar balla tagogin dakunan dake kulle.

Shi dai wannan makaranta an kafata ne tun kafin samun yancin kai, a shekarar 1954, kuma ta fara koyar da dalibai ne a kusa da asibitin Dutse dake unguwar tudun wada cikin garin Kaduna.

Gobara ta tafka ma dalibai mummunan asara a wata babbar makaranta dake Kaduna
Kwalejin Makarfi
Asali: Facebook

Kwalejin tana horas da dalibai akan ilimin jinya, karbar haihuwa, kiwon lafiya, tsatafe muhalli, kimiyyar daukan hoton sassan jiki, da dai sauran jami’an da ake bukata a fannin kiwon lafiya, musamman a Asibitoci, amma a matakin karamin difloma.

Sai dai daga bisani kwalejin ta samu habbaka, inda a yanzu haka tana bada babbar difloma ga dalibanta bayan sun yi aikin samun horo, sanin makaman aiki da kuma gogewa a asibitoci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel