Mataimakin Gwamnan Kaduna ya na sa rai Buhari da El-Rufai za su zarce a 2019

Mataimakin Gwamnan Kaduna ya na sa rai Buhari da El-Rufai za su zarce a 2019

Mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Barnabas Bala Bantex, ya bayyana cewa yana sa ran Mai gidan sa gwamna Nasir El-Rufai da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari za su yi nasara a zaben bana.

Mataimakin Gwamnan Kaduna ya na sa rai Buhari da El-Rufai za su zarce a 2019

Lokaci APC ta ke jira ta jin ance ta ci zaben 2019 inji Bantex
Source: Facebook

Arch. Barnabas Bala Bantex ya bayyana wannan ne a jiya Asabar 12 ga Watan Disamba a lokacin da yake yawon yakin neman zabe a Garin Zonkwa da ke cikin karamar hukumar Zangon Kataf a yankin Kudancin jihar Kaduna.

Bala Bantex wanda yanzu haka yake yakin neman kujerar Sanata a yankin sa na kudancin Kaduna yake cewa jama’a za su zabi gwamnan jihar na Kaduna da kuma shugaban kasa Buhari saboda irin ayyukan da su kayi a ka kuma gani.

KU KARANTA: 2019: Ta gama karewa Jam'iyyar PDP a Najeriya inji Osinbajo

Mataimakin gwamnan ya fi ganin cewa manyan ‘yan takaran na APC za su kai labari a zaben da za ayi a watan gobe. Arch. Bala Bentex yace ba ya ko tunanin cewa Muhammadu Buhari da El-Rufai za su sha kasa a zaben da za ayi.

Kamar yadda mu ka ji, mataimakin na El-Rufa’i ya fadawa jama’an Garin Zonkwa cewa lokacin kurum su ke jira su ji hukumar INEC ta sanar da nasarar shugaban kasa Buhari da gwamnan jihar domin su zarce a kan karaagar mulki.

‘Dan takarar na Sanatan Kaduna ta kudu a majalisar dattawa ya kuma yi kira ga mutanen Yankin da su fito kwan-su-da-kwarkwata wajen ganin sun ba sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC mai mulki goyon bayan da su ke bukata a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel