An sake gwabza hadari a hanyar Legas, da yawa sun mutu

An sake gwabza hadari a hanyar Legas, da yawa sun mutu

- Mutane Uku sun rasa rayukan su yayin da wasu kuma suka jikkata

- Hatsarin ya afku ne a babbar hanyar dake tsakanin Legas da Ibadan

- Tayar motar ta fashe a lokacin da direban yake tsaka da sharara gudu akan hanya

An sake gwabza hadari a hanyar Legas, da yawa sun mutu

An sake gwabza hadari a hanyar Legas, da yawa sun mutu
Source: Original

Mutane Uku ne suka rasa rayukan su yayin da mutum 11 kuma suka samu munanan raunuka a yayin wani hatsarin mota da akayi.

Hatsarin ya afkune a ranar Juma'a a kusa da Makun a babbar hanyar dake tsakanin Legas da Ibadan.Hatsarin ya afkune a ranar Juma'a a kusa da Makun a babbar hanyar dake tsakanin Legas da Ibadan.

Mr Clement Oladele shugaban hukumar kiyaye hadarurruka FRSC ta jihar Ogun ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Asabar.

GA WANNAN: Manyan barayi na can na neman quri'u, kanana na can suna shan dauri

Tayar motar ta fashe a daidai lokacin da direban yake tsaka da sharara gudu akan titi.

Maza Uku da mata Takwas sun samu raunuka yayin da namiji daya da mata Biyu suka rasa rayukan su.Maza Uku da mata Takwas sun samu raunuka yayin da namiji daya da mata Biyu suka rasa rayukan su.

Jami'in FRSC ya bayyana cewa an kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti yayin da aka mika gawarwakin wadanda suka rasu zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Olabisi Onabanjo( OOUTH) Sagamu.

Daga karshe ya shawarci masu tuki dasu dunga duba lafiyar tayoyin motar su da kuma fitilun motar su saboda karancin haske.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel