Sau hudu ina tsallake yunkurin kashe ni - Tsohon gwamnan PDP a arewa

Sau hudu ina tsallake yunkurin kashe ni - Tsohon gwamnan PDP a arewa

A jiya ne tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, ya bayyana yadda a karo hudu ya tsallake yunkurin kashe shi saboda dagewar sa a kan a yiwa jama'ar jihar sa da ma Najeriya adalci.

Tsohon gwamnan ya ce an fara yunkurin kashe shi ne saboda sukar gwamnati da ya yi a lokacin da rikicin Boko Haram ya yi zafi a yankin arewa maso gabas.

Nyako ya bayyana cewar harkar tsaro ta matukar lalacewa a shekarar 2014, hakan da kuma hadi da barazanar da ake yiwa rayuwar sa sun saka shi barin Najeriya, amma duk da haka bai daina kira ga jama'a a kan bukatar su zauna lafiya ba.

Sau hudu ina tsallake yunkurin kashe ni - Tsohon gwamnan PDP a arewa
Murtala Nyako
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na wadannan kalamai ne yayin karbar wasu magoya bayan jam'iyyar SDP karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar Mayo Belwa, Ishaku Barnabas, da suka ziyarce shi a gidansa dake Yola, babban birnin jihar Adamawa, domin bayyana masa canjin shekar su zuwa jam'iyyar ADC.

DUBA WANNAN: Matasa sun wanke titi da sabulu bayan ziyarar El-Rufa'i, hotuna

Ya shaida masu cewar nan bada dadewa ba jam'iyyar ADC zata kafa kwamitin tuntuba a kananan hukumomin jihar Adamawa.

Kazalika ya bukaci matasa da kar su bari 'yan siyasa suyi amfani da su domin bangar siyasa tare da yin kira garesu su rungumi harkar noma domin samun damar dogaro da kansu da kuma bayar da gudunmawa wajen gina tattalin arzikin kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel