An haramta amfani da mayukan bilicin masu haskaka fata a kasar Rwanda

An haramta amfani da mayukan bilicin masu haskaka fata a kasar Rwanda

- Kasar Rwanda ta haramta samar da duk wani man shafawa ko sabulu mai sanya haske a kasar

- Da yawa daga cikin kasashen Afurika sun haramta samar da irin wadannan mayuka amma basu tsaurara doka akai ba

- Shugaban kasar ta Rwanda ya nuna damuwar sa akan yawaitar abubuwan dake sanya hasken

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Source: UGC

Kasar Rwanda ta haramta samar da mayuka da sabulai dake sanya hasken fata a kasar.

Ta bayyana haka ne a wani sakon yaki da abubuwa masu sanya hasken fata data tura mai taken "Love the skin you are in".

An haramta amfani da mayukan bilicin masu haskaka fata a kasar Rwanda

An haramta amfani da mayukan bilicin masu haskaka fata a kasar Rwanda
Source: Twitter

Wani jami'in hukumar lafiya ta kasar mai suna Francois Uwinkindi yace " Mun mayar da hankali akan fadakar da al'umma akan wannan abu da kuma kwace wadannan kayayyaki,muna munbi bayan ragowar kasashen da suke yaki d wadannan kaya masu canja launin fata.

Shugaban kasar na Rwanda Paul Kagame ya nuna damuwar sa akan bunkasar irin wadannan kaya a cikin al'umma.

An bayyana cewa jami'an yan sanda a kasar sun fara kwace irin wadannan kaya tun a satin karshe na shekara ta 2018.

DUBA WANNAN: Matsalar shaye-shayen mata ta fara sauki a Kano, sai dai, Katsina ta dauka

Amma da dama daga cikin masu amfani da wadannan abubuwa basuyi farin ciki da wannan doka ba inda sukace suna da damar zabawa kansu abinda sukaga zasuyi.

Da yawa daga cikin kasashen Afurika sun haramta samar da ire iren wadannan abubuwa amma basu sanya doka akan hakan ba, wadannan kasashe sun hada da Ghana, Afrika ta kudu, Mali da kuma Najeriya.

A shekarar data gabata ne Blac Chyna dake Amurka suka kawo wani sabon samfurin mai dake kara hasken fata zuwa kasar Najeriya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel