Hukuma tayi holin 'yan ta'adda bakwai a jihar tsakiyar Najeriya

Hukuma tayi holin 'yan ta'adda bakwai a jihar tsakiyar Najeriya

- Yan sandan jihar Benue sun gurfanar da yan ta'adda 7 a gaban kuliya

- Ana zargin su da laifin hadin kai gurin aikata laifukan garkuwa da mutane da karbar kudin fansa

- Sojojin rundunar 707 ne suka cafko su

Hukuma tayi holin 'yan ta'adda bakwai a jihar tsakiyar Najeriya

Hukuma tayi holin 'yan ta'adda bakwai a jihar tsakiyar Najeriya
Source: UGC

Hukumar yan sandan jihar Benue a ranar talata ta gurfanar da mutane bakwai gaban babban kotun ta II ta yankin Makurdi da ake zargi da hadin kai gurin aikata laifi da ta'addanci.

Wadanda ake zargin sune: Godwin mai shekaru 26, Akan Pevelga mai shekaru 28, Eric Azanye, Richard Aaser mai shekaru 35, Luter Pev mai 22, Gwaza Ukuma mai shekaru 33 da kuma Justine Yangedu mai shekaru 30.

Wadanda ake zargin duk manoma ne a gurare daban daban na kananan hukumomin Ukum da Katsina-Ala.

Mai kara sifeto Veronica Shagee, ta sanar da kotu cewa wadanda ake zargin rundunar soji ta 707 na Zaki-Biam dake karamar hukumar Ukum na jihar Benue ne suka cafkesu.

Mrs Shagee tace a karshen 2018 ne sojojin suka samu labarin aiyukan ta'addanci da kungiyar suke yi a garin.

Wacce ke karar tace sojojin sunyi binciken zargin da ake ma mutanen inda daga baya suka cafke su a maboyar su.

Mrs Shagee tace kungiyar, wadanda ke aiyukan su a matsayin yan kungiyar cigaban matasan Mbamena, ana zargin su da sace mutane tare da garkuwa dasu da kuma neman kudin fansa.

DUBA WANNAN: Shugaban Bankin Duniya yayi mubabus na bagatatan babu dalili

Tace an maida su ga DSS Makurdi inda daga baya suka kai su ga yan sanda don cigaba da bincike tare da hukunci.

Mai karar tace laifukan sun ci karo da sashi na 8 da na 1, sakin layi na biyu na dokokin hana ta'addanci da aka gyara a 2013.

Kotun ta ki sauraren rokon wadanda ake zargi saboda bata da karfin yanke hukunci.

Mai shari'a, Rose Iyorshe ta bada umarnin cigaba da tsare wadanda ake zargin a gidan kaso kuma ta daga sauraren karar zuwa 11 ga watan Fabrairu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel