Fillo yaki Fillo: Miyetti Allah tace ayi wa Allah kada a zabi Atiku

Fillo yaki Fillo: Miyetti Allah tace ayi wa Allah kada a zabi Atiku

- Kungiyar Miyetti Allah ta hori yan Najeriya da kada su zabi Atiku

- Shugaban kungiyar ya zargi Atiku da amfani da rahoton A1 don bata musu suna

- Tuni gwamnatin tarayya ta karyata rahoton da A1 ta saka a watan Disamba

Fillo yaki Fillo: Miyetti Allah tace ayi wa Allah kada a zabi Atiku
Fillo yaki Fillo: Miyetti Allah tace ayi wa Allah kada a zabi Atiku
Asali: Depositphotos

Kungiyar Miyetti Allah ta hori yan Najeriya da kada su zabi Atiku Abubakar, Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben watan Fabrairu mai zuwa.

Shugaban kungiyar na kasa,Bello Bodejo, yayi wannan kiran a taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis.

Ya zargi Mista Atiku da kokarin hargitsa kasar da rahoton fadan manoma da makiyaya da A1 ta saki a watan Disamba.

A rahoton da aka saki a watan Disamba, kungiyar tace fadan yayi ajalin rayuka 3,641 a shekaru uku da suka gabata.

Kungiyar tace kisan yana karuwa ne sakamakon cewa cibiyoyin da ya kamata basa yin bincike tare da zakulo masu hannu a ciki da hukunta su, zargin da gwamnatin tarayya ta karyata.

"Atiku ya jinjina rahoton don suka ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan gazawar ta wajen kare rayukan mutane."

Miyetti Allah ta taso kan maganar tsohon mataimakin shugaban kasar inda ta kwatanta abinda yake da "Rawa tsirara a kasuwa" .

"Mun kushe gaggawar Atiku na amfani da rahoton karya da burin cimma nasarar siyasa akan fadan manoma da makiyaya. Muna kira ga yan Kungiyar mu da kuma masu son zaman lafiya a Najeriya da kada su saurari tsoki burutsun shi sannan kuma kada su zabe shi. Mun fadi haka ne saboda bashi da burin cigaba da kuma zaman lafiya a kasar Nan."

DUBA WANNAN: Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata

Shugaban kungiyar yace duk laifin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne da ta jawo mutum irin Atiku a matsayin mataimakin shi ,yanzu kuma gashi yana son hayewa kujerar shugabancin kasar.

Kamar yadda suka zarga, Dan takarar PDP din na zagaye da mutanen da suka tsani Fulaniy kuma suke munanan kalamai garesu tare da kiran musu zubda jini.

Mista Badejo yayi kira ga Buhari da ya sa jami'an tsaro su sanya ido akan Atiku saboda kalaman da yake yi ga makiyaya.

"Kalaman shi a matsayin Dan takarar shugabancin kasa zai iya kawo hargitsi a kasar."

Kungiyar ta kushe A1 akan rahoton karya da ta saki wanda tace don cika umarnin wanda ya biya su ne.

Shugaban yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta lura da aiyukan A1 balle yanda take samun kudi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel