An dakatar da 'yan majalisun Zamfara guda 4 saboda tuburewa Gwamna Yari

An dakatar da 'yan majalisun Zamfara guda 4 saboda tuburewa Gwamna Yari

- Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da mambobinta guda hudu a kan zarginsu da rashin da'a da biyaya ga gwamnati da majalisar

- Wadanda aka dakatar sune Hon. Mansur Musa Bungudu, Hon. Mani Malam Mummuni, Hon. Abdullahi Dansadau, da Hon. Salisu Musa Tsafe

- Majalisar ta kafa kwamitin bincike na wucin gadi da zai bincika zargin da ake yiwa 'yan majalisar kafin daukan mataki

A jiya, Alhamis ne majalisar jihar Zamfara ta dakatar da mambobinta hudu da ke zarginsu da goyon bayan bangaren jam'iyyar ta APC mai suna G-8 da ke karkashin jagorancin mataimakin gwamna Ibrahim Wakkala da Sanata Kabiru Marafa da Ministan Tsaro Mansur Dan-Ali da sauransu.

An dakatar da 'yan majalisun Zamfara guda 4 saboda tuburewa Gwamna Yari
An dakatar da 'yan majalisun Zamfara guda 4 saboda tuburewa Gwamna Yari
Asali: UGC

'Yan majalisar da aka dakatar dai sun hada da Hon. Mansur Musa Bungudu, Hon. Mani Malam Mummuni, Hon. Abdullahi Dansadau, da Hon. Salisu Musa Tsafe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: INEC ta bayar da muhimmiyar sanarwa a kan zaben 2019

A taron gagawar da majalisar ta kira a jiya, Jagoran majalisar Hon. Isa Abdulmunin ya bukaci majalisar da dakatar da mambobin saboda abinda ya kira "rashin da'a da biyaya ga gwamnati da shugabancin majalisar."

Ciyaman din kwamitin Ilimi na majalisar, Hon. Kabiru Moyi Birnin Magaji ya tabbatarwa majiyar Legit.ng dakatarwar.

Ya ce majalisar ta kafa kwamitin bincike na wucin gadi da zata duba ayyukan da 'yan majalisar suka kasance suna yi, ba za su dawo majalisa ba har sai an samu sakamakon da kwamitin binciken ta fitar.

Kakakin majalisar, Hon. Sanusi Garba Rikiji ne ya sanar da dakatar da 'yan majalisar.

A baya, gwamnatin jihar ta dakatar da mataimakan ciyamomin kananan hukumomi uku saboda alakarsu da mambobin G-8. Kananan hukumomin sune Zurmi, Birnin-Magaji da Gummi.

Mataimakin ciyaman din karamar hukumar Zurmi, Alhaji Abubakar Dauran ya ce ba dai-dai bane a sallame su saboda banbancin ra'ayi tunda dai sun 'yan jam'iyya ne masu biyaya ga dokokin jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel