Shegen wayau gare ni, shi yasa 'yandoka suka kasa kama ni har yanzu

Shegen wayau gare ni, shi yasa 'yandoka suka kasa kama ni har yanzu

- Melaye yace buyar da yakeyi ba tsoro bane, hikima ce

- Ya kwatanta kanshi da Annabi Iliyasu na cikin Bible da ya boye a tsaunin Carmel yayin da Sarki Ahab ke bibiyar shi

- Yan sanda sunce ba gudu ba ja da baya, sai sun kama shi zasu bar gidanshi

Shegen wayau gare ni, shi yasa 'yandoka suka kasa kama ni har yanzu
Shegen wayau gare ni, shi yasa 'yandoka suka kasa kama ni har yanzu
Asali: Twitter

Sanata Dino Melaye a jiya yace ba zai mika kanshi ga hukumar yan sandan Najeriya ba cewa da buyar da yakeyi fasaha ce ba tsoro ba.

Mahukuncin mai wakiltay jihar Kogi ta yamma ya zargi yan sanda da tsara yanda zasu karya kofofin gidan shi don su kama shi ta karfi.

Melaye, wanda ke takarar komawa kujerar shi karkashin jam'iyyar PDP,a shafin shi na tuwita ya danganta kalubalen da ya fuskanta da irin na Annabi Iliyasu a Bible.

"Bible ya bada labarin Annabi Iliyasu a matsayin daya daga cikin karfafan annabawa da ya taba rayuwa, amma yaje tsaunin Carmel don boyewa daga yunkurin kisan sarki Ahab saboda yanda yake fadin gaskiya ba tsoro. Akwai bambanci tsakanin tsoro da wayau."

Sanatan yace yan sandan suna tafe ne da motar Yan sanda wacce sukayi niyyar balle kofofin shi da ita.

"Yan sanda sunzo da motar EOD don karya kofofin da rushe min gidana." Amma yan sanda sun musa zargin kuma sun dau manema labarai inda suka zagaye gidan don tabbatar da hakan.

DUBA WANNAN: Kasashen da jarirai ke son a haife su da inda bassu so a 2019

Jami'an tsaron sun tura karin yan sanda don kama sanatan wanda tuni suke zageye da gidanshi dake layin Sangha a Maitama, Abuja.

A yau dai kwanaki 6 kenan da kungiyar yan sanda suka zagaye gidan sanatan don kama shi akan laifin zargin "ta'addancin hadin kai da kisan kai da yayi a 19 ga watan Yuli, 2018."

Yan sandan sun ce ana zargin mahukuncin ne da harbin wani Sajan Danjuma Saliu mai aiki a 37 Police Mobile Force wanda yake aikin tsayarwa da duba ababen hawa a hanyar Aiyetoro Gbede, titin Mopa a jihar Kogi.

Melaye, da yayi ikirarin baya Abuja yace wa Yan sandan suyi tsaron kasar a maimakon neman shi, yace "Ni ba Dan ta'adda bane kamar yanda yan sanda ke zargi."

Yan sandan sun ce sunji shi yayi ihu ga wani jami'i daga tagar saman gidan shi.

Yan sandan sun tsinke hanyoyin wutar lantarkin gidan a matsayin hanyar takura shi har ya fito amma sanatan yaki.

Mai magana da yawun yan sanda, Jimoh Moshood yace Melaye ya samu gayyata marasa adadi don yazo ayi binciken kisan kai da ake zargin shi amma yaki zuwa. Yace yan sandan bazasu bar gidan mahukuncin ba ba tare da sun kamashi ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel