Kasashe biyar a fadin duniya da suka fi shan wahalar ta'addanci a 2018

Kasashe biyar a fadin duniya da suka fi shan wahalar ta'addanci a 2018

- Wani bincike ya bayyana kasashen da sukafi kowanne fama da ta'addanci

- A cikin jerin kasashen Biyar Najeriya ce tazo ta Uku

- Sannan wadannan kasashe sunfi kowanne yawan al'umma

Kasashe biyar a fadin duniya da suka fi shan wahalar ta'addanci a 2018
Kasashe biyar a fadin duniya da suka fi shan wahalar ta'addanci a 2018
Asali: UGC

Wani bincike da aka gudanar ya fitar da kasashen da sukafi kowanne yawan al'umma da ta'addanci.

Binciken ya rattabu kasashe guda Biyar dake fama da matsalar ta'addanci inda Najeriya tazo a kasa ta Uku a wannan fagen.

Duk da cewa Boko Haram tafi kashe mutane a fadin duniya a shekarun 2013 da 2014, a yanzu kam, a kasashen Syria/Iraqi, Somalia da Afghanistan da ma Pakistan ne ake samun wannan matsala ta tsaro. Sai dai kuma, kamar Boko Haram din ta dawo.

DUBA WANNAN: Abubuwan da Allah zai yi da Najeriya a bana 2019 - kungiyar CAN

Kamar yadda muka sani cewa kasar Iraq tana fama da rashin kwanciyar hankali tun 1991, da 2003, bayan da Amurka ta tumbuke Saddam Hussaini daga mulki, binciken ya sanya ta a kasa ta farko inda take dauke da kaso 9.746.

Yayin da kasar Afghanistan ta biyo bayan ta da kaso 9.391.

Sai kasar Najeriya inda take da 8.660.

Syria tana da 8.315

Kasar Pakistan tana dauke da 8.181.

Kamar wanda lissafin ya bayyana wadannan kasashe suna daga cikin kasashen dake da tarin al'umma a cikin su. Kuma dukkaninsu na musulmi ne.

Sauran kasashe dake shan wahalar ta'addanci da basu kai wannan girma ba sun hada da Palestinu, wadanda ke neman kasar kansu, sai Libya, da Somaliya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel