Hatsarin jirgin yaki: Rundunar sojin sama ta sanar da mutuwar mutum 5

Hatsarin jirgin yaki: Rundunar sojin sama ta sanar da mutuwar mutum 5

Hukumar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta sanar da cewa matukan jirginta biyu da wasu sojoji uku ne suka rasu sakamakon hatsarin jirgi mai saukan angulu yayi a daren Laraba yayin yaki da Boko Haram.

Sun ta ruwaito cewa jirgin mai saukan angulu kirar Mi-35M ya yi hatsari ne yayin da ya ke tallafawa dakarun sojin Najeriya na Bataliyar 145 a garin Damasak da ke jihar Borno.

Mai magana da yawun sojin saman Najeriya, Air Commodre Ibikunle Daramola ya bayyana sunayen wadanda suka rasu kamar haka, Flight Laftanat Perowei Jacob; Flight Laftanat Kaltho Paul Kilyofas; Saja Auwal Ibrahim; Lance Corporal Adamu Nura da Meshack Ishmael.

Hatsarin jirgin yaki: Rundunar sojin sama ta sanar da mutuwar mutum 5
Hatsarin jirgin yaki: Rundunar sojin sama ta sanar da mutuwar mutum 5
Asali: Facebook

Sanarwar ta Daramola ta ce: "Ina son amfani da wannan damar domin sanar da rasuwar sojoji 5 da ke cikin jirgi mai saukan angulu na NAF kirar Mi-35M da ya yi hatsari a jiya 2 ga watan Janairu yayin da ya ke taimakawa dakarun bataliyar 145 yaki a Damasak a jihar Borno."

Ya ce tuni an kwashe gawarwakin dakarun sojin an tafi da su Maiduguri.

"Wadannan jaruman sojojin sun sadaukar da rayuwarsu wurin yiwa kasarsu hidima, hakan yasa hukumar sojin sama da ma dukkan 'yan Najeriya ba za su taba mantawa da su ba.

"A madadin dukkan sojoji da ma'aikatan NAF, shugaban hafsin sojojin sama na kasa, Air Marshal Sadique Abubakar, yana mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan sojojin kuma yana addu'ar Allah ya gafarta musu."

"NAF tana godiya bisa goyon bayan da 'yan Najeriya ke nuna mata. Muna bukatar goyon baya daga gare ku a yayin da muke kokarin tsare Najeriya da 'yan Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel