Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da na hannun damar Ganduje daga mukaminsa

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da na hannun damar Ganduje daga mukaminsa

- Majalisar Jihar Kano ta dakatar da shugaban KASCO na jihar Kano, Alhaji Bala Inuwa

- Majalisar da dakatar da Bala Inuwa ne saboda ya ki amsa kirar majalisar na zuwa ya kare kasafin kudin hukumar

- Hukumar KASCO ita ke da alhakin samarwa manoman Kano dukkan kayayakin noma da suke bukata

A ranar Litini ne majalisar jihar Kano ta dakatar da babban manajan kamfanin samar da kayayakin Noma na Kano (KASCO), Alhaji Mohd Bala Inuwa saboda rashin bayyana gabanta domin kare kasafin kudin ma'aikatarsa.

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da na hannun damar Ganduje daga mukaminsa

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da na hannun damar Ganduje daga mukaminsa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

Kakakin majalisar na jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurun ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Litinin, jim kadan bayan kwamitin majalisar ta gama tattaunawa kan wasu muhimman abubuwa.

Rurum ya ce majalisar ta dakatar da shugaban na KASCO ne saboda ya ki bayyana gaban kwamitin majalisar na ayyukan noma domin kare kasafin kudin hukumarsa na shekarar 2019.

"Duk da kokarin da kwamitin tayi na kiran shugaban na KASCO domin ya bayyana gaban kwamitin, ya ki amsa wayarsa," inji Kakakin majalisar.

Kakakin majalisar ya kara da cewa rashin bayyanar shugaban na KASCO ya sanya 'yan majalisar sun amince ba za su bawa hukumar ko kwandala ba a kasafin kudin na 2019.

KASCO ita ke da alhakin samarwa dukkan manoman Kano da taki da sauran kayayakin noma har ma da wasu johohin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel