ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

- Kungiyar ISIS tayi barazanar janye tallafin makamai da kudi da ta ke bawa kungiyar Boko Haram

- ISIS za ta dauki wannan matakin ne sakamakon gazawar Boko Haram na kafa daular musulunci a Najeriya cikin wa'addnin shekaru uku

- An ganin cewar janyewar tallafin da ISIS ke bawa kungiyar ta Boko Haram zai kassara kungiyar domin za su rasa babban hanyar samun tallafinsu

Kungiyar ta'addanci na kasa da kasa, Islamic States West African Province (ISWAP-ISIS) tana shirin korar Boko Haram daga cikin ta domin ta gaza kafa daular musulunci a yankin arewa maso gabashin Najeriya kamar yadda wata rahoton ta bayyana.

Binciken da kungiyar sanya ido a kan ayyukan ta'addanci na kasa da kasa (ITMG) ya bayyana cewar an bawa kungiyar Boko Haram wa'addin shekaru uku su kafa daular musulunci a Najeriya.

Sai dai ITMG ta ce ISIS tana gab da raba jiha da kungiyar Boko Haram saboda gaza kafa daular musuluncin cikin wa'addin da aka diba mata.

ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya
ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya
Asali: Getty Images

Rahoton na ITMG ya ce: "ISIS tayi barazanar korar Boko Haram saboda sun bari sojojin Najeriya sun kwace garuruwan da suka da ikon a kansu a baya kamar Camp Zero da ke dajin Sambisa da garuruwan Kukawa, Baga da yunkunan tafkin Chadi da kasar Nijar."

DUBA WANNAN: Wani da ya yiwa kanwarsa mai shekaru 15 ciki a Kano ya dora laifi kan shaidan

Har ila yau, rahoton ya ce akwai yiwuwar Boko Haram ta zo karshe kenan saboda galibin tallafin makamai da sauran kayan yaki da take samu yana zuwa ne daga ISIS.

"Cikin yarjejeniyar da Boko Haram su kayi da ISIS shine samun makamai. Yanzu za a yanke basu tallafin makaman wanda hakan na nufin karshen kungiyar ya zo kusa."

Rahoton ya kara da cewa sabbin hare-haren da mayakar na kungiyar Boko Haram suke kaiwa kwana kwanan nan ba zai rasa alaka da wa'addin da aka basu ba barazanar korar su daga ISIS muddin ba su kafa daular musuluncin ba.

"Daya daga cikin dalilin da yasa 'yan ta'addan ke tsananta hare-hare shine yana da nasaba da babban zabe mai zuwa, idan hare-haren ya tsananta hakan zai sa ba za ayi zabe a yankin ba.

Amma a halin yanzu, Boko Haram ta gaza kwace iko a kan ko wanne gari a shekaru uku da suka gabata ba kamar yadda suka kwace kananan hukumomi 16 ba a yankin arewa maso gabas a zamanin gwamnati na baya," inji rahoton.

Kamar yadda kungiyar ta ISIS ta saba, tana tsayar da bayar da tallafi ga duk wata kungiya da ke karkashinta da ta gaza kafa daula a cikin shekaru uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel