Ko N500 daya babu a jikin Alex Badeh sanda ya rasu, iyalansa sun karyata 'yansanda

Ko N500 daya babu a jikin Alex Badeh sanda ya rasu, iyalansa sun karyata 'yansanda

- Iyalan Badeh sun musa ikirarin wadanda ake zargi da kisan shi

- Sunce labarin kagagge ne kuma kirkirarre

- Bashi da ko sisi a ranar da aka kashe shi

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Source: Twitter

Iyalan marigayi Air Vice Marshal Alex Badeh sun musa ikirarin daya daga cikin wadanda ake zargi da kisan marigayin cewa tsohon shugaban sojin yana hanyar shi ne ta zuwa jihar Nasarawa ne don siyan gona da wasu makuden kudade.

Idan zamu tuna, wadanda ake zargin a yayin da suke sanar da yan sanda sunce marigayin na kokarin kai wasu makuden kudade ne don siyan wani fili a jihar Nasarawa, wanda su tsarin su shine su tare shi tare da kwace kudin.

Amma kuma daya daga cikin iyalan shi da yayi magana da majiyar mu yace: "Mu a matsayin mu na iyalan shi, mun yarda cewa wasu ne suka shirya kisan shi, suke so su yaudari jama'a ta hanyar boye ainihin abinda ya faru, yanda ya faru da kuma su waye suka aiwatar."

"Ina so in sanar daku cewa hakan yaci karo da abinda ya faru na cewa da akayi ya I tafi da kudi makudai ne don siyan gona, babu wani abu makamancin hakan. A takaice ma babu kudi a jikin shi ranar, ko N500 kuwa babu a motar."

"Kafin mutuwar shi, wani bakauye yaje gurin shi a gona don samun kudi da zai siya maganin ciwon kai Wanda bai da halin siye. Sai yace ma mutumin ko zai iya zuwa kasuwar Panda? Sai mutumin yace zai iya.

Sai yace dan'uwan mu ya debo ma mutumin mudu goma na masara, yaje ya siyar sai ya samu na magani don bashi da kudi a tare dashi. Har ma ya kara ma mutumin bayanin cewa Yana da shara mai tarin yawa a gidan shi a Abuja amma masu alhakin kwashewa sunki kwasheta saboda bashi da kudin biyane su.

Ya Kara da cewa bai biya kuku da mai sharar gidan shi ba saboda bashi da kudi. A saboda ma haka ne ma yaje kasuwa ranar don samun koda buhu 100 na masaray don ya siyar ya biya bukatun shi."

DUBA WANNAN: Ko iyalan Buhari da gaske sun sayi Etisalat? Ga yadda batun yake

"Sannan kuma ya sanar da ma'aikata da sukayi mishi aiki a gona cewa tunda an toshe fansho din shi, mutane uku cikin takwas dake mishi aiki ne zai iya biya don haka kada biyar din su fara aikin. Masarar shi zai dinga siyarwa don biyan sauran ukun da zasu yi aikin."

"Bashi da ko dari biyar na rantse da ubangiji a ranar da akae kashe shi. Kawai kirkirarren labari suke fada muku."

"Yaje gonna ne don samun masarar da zai siyar ya biya kuku,mai shara da kuma masu kwashe shara. Kalli sharar dake can. An matsar da ita ne don warin na damun waccan makarantar firamaren. Toh ta ina suka samu labarai da suke fada wa mutane?"

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel