Duk da zargin rashawa, Nyako yace ya tsaya ma dansa kan batun takarar gwamna

Duk da zargin rashawa, Nyako yace ya tsaya ma dansa kan batun takarar gwamna

- Baba mai mangoro ya fito don tsaya ma Dan shi

- Gwamnatin tsohon gwamnan jihar Adamawa dama ta mutane ce

- Bindow yayi alkawarin dasa wa daga inda tsohon gwaman ya tsaya amma ya kasa

Duk da zargin rashawa, Nyako yace ya tsaya ma dansa kan batun takarar gwamna
Duk da zargin rashawa, Nyako yace ya tsaya ma dansa kan batun takarar gwamna
Asali: Twitter

Tsohon gwamna Murtala Nyako zai tsaya was Dan shi, sanata Abdulazeez Nyako wanda ke takarar kujerar shugabancin jihar Adamawa karkashin jam'iyyar ADC.

Ofishin dillancin labarai sun tuna cewa Abdulazeez sanata ne dake wakiltar jihar Adamawa ta tsakiya, ya bar jam'iyyar APC zuwa ADC inda yayi nasarar samun tikitin takarar kujerar gwamnan jihar.

Shugaban jam'iyyar na jihar,Alhaji Yahaya Hamman Julde, ya sanar da hakan a yayin taron shi da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Toungo ta jihar Adamawa.

Hamman Julde yace mulkin Nyako sananne ne ga mutanen jihar sakamakon shirye shiryen shi duk na mutane ne.

Kamar yanda yace, gwamnatin zata kawo karshen matsalar talauci tun daga tushe a don haka ne mutane ke ta son dawowar su saboda suna da tabbacin sanata Abdulazeez zai dawo da shirye shiryen nan idan aka zabe shi.

Shugaban jam'iyyar yace yawancin yan jam'iyyar ADC har da sanata Nyako masu fushi ne da jam'iyyar APC wadanda suka yi kokariny ganin nasarar jam'iyyar a zaben 2015 a jihar amma ta kasa tabuka abin azo a gani.

DUBA WANNAN: Bayanan da muke samu daga Baga

"Matasan mu da manoman mu na karkara suna bukatar shirye shiryen gwamnatin Nyako kamar su Local Apprenticeship Scheme da Farming Skills Acquisition centres da suke habaka noman manoma da sauran su. Mun hadu da talakawa mun ture gwamnatin PDP don saka gwamna Muhammadu Bindow karkashin jam'iyyar APC, wanda yayi alkawarin farfado mana shirye shirye masu amfani amma ya kasa cika alkawarin. Yanzu gamu muna bada hakurin laifin shi tare kuma da kawo muku madadin shi da muke da tabbacin ba zai kasa cika alkawarin ba. Mahaifin shi sananne ne kuma yayi alkawarin tsaya mishi. Kunfi sanin shi da Baba Mai mangoro."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel