Shugaba Buhari na ta'aziyya ga Katsina kan rasuwar malaminsa

Shugaba Buhari na ta'aziyya ga Katsina kan rasuwar malaminsa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta'aziyyar malamin shi

- Wannan babban rashi ne garemu, jihar Katsina da mutanen ta

- Kwazon shi ne zamuyi ta tunawa tare da jajircewar shi

Shugaba Buhari na ta'aziyya ga Katsina kan rasuwar malaminsa
Shugaba Buhari na ta'aziyya ga Katsina kan rasuwar malaminsa
Asali: Depositphotos

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar alhamis yayi ta'aziyyar malamin shi Alhaji Sanda Kaita, Magajin Rogon Katsina, tsohon malamin shi.

A sakon ta'aziyyar ga sarkin Katsina, gwamnatin da mutanen jihar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta malamin nashi na darasin aiyukan karafa a makarantar sakandare ta Katsina da mutum mai kyawun halayya wanda za'a dinga tuna shi da aiyukan kwazo da ya koyar da daliban shi.

"Malami ne mai kwazo da maida hankali. Addu'o'in mu na ga iyalan da ya bari, gwamnati da kuma mutanen jihar Katsina akan wannan rashin da sukayi. Muna fatan ubangiji yayi mishi gafara," inji shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Kudin da muke rabo na bashi da wata alaka da neman tazarce - Farfesa Qanen shugaba Buhari

A baya dai, an ta cewa shugaba Buhari bayyi makaranta ba, lamari da ya kai sai da shugaban ya ce aje a tambaya a makarantarsa, kuma ma yace tare da su Shehu 'yarAduwa yayi, shi kuwa Principal din, ya wanke shi tsaf ya mara masa baya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel