Gaskiyar magana kan zargin wai ko iyalan Buhari ke da Etisalat da bankin Keystone

Gaskiyar magana kan zargin wai ko iyalan Buhari ke da Etisalat da bankin Keystone

- Atiku yace kamfanin sadarwa na etisalat da bankin Keystone mallakin yan uwan Buhari ne

- Bankin Keystone na karkashin babban bankin Najeriya ne

- Babu mahalukin da ya isa ya mallaki bankin da aka siyar

Talakawan dangin Buhari sun zamo biloniyoyi daga hawansa mulki - Buba Galadima
Talakawan dangin Buhari sun zamo biloniyoyi daga hawansa mulki - Buba Galadima
Asali: UGC

Atiku Abubakar na ta fusata kuma hakan ke sa yake ganin abubuwa ba yanda suke ba. Ya zargi cewa yan uwan shugaban kasa Muhammadu Buhari ne mamallakan kamfanin sadarwa na etisalat da bankin Keystone.

Yayi nasarar saka wannan zargin a zuciyoyin magoya bayan shi. Bari muyi bayani saboda shi da magoya bayan shi

*Babu wani abu wai shi etisalat. Mamallakan etisalat sune kungiyar mubadala daga Abu Dhabi ,UAE. Mamallaki kuma shugaban kungiyar shine Hakeem Bello Osagie wanda ya siya mafi yawan hannun jarin kamfanin sadarwa na etisalat wanda ya kai ga siyar da yawan hannayen jarin shi na UBA ga Tony Elumelu da kungiyar masu hannayen jarin shi.

Ya siyar da hannayen jarin shi na kusan Naira biliyan 10 a 2002 lokacin da Obasanjo da Atiku Abubakar suka siyar da hannayen jarin gwamnatin tarayya na UBA. Kungiyar mubadala sun bar kamfanin sadarwa na etisalat ne saboda rashin kwarewar kamfanin a aiyukan shi da kuma basussukan da ke saka bankuna cikin wani hali.

*Bankin Keystone kuwa ba a siyarwa da kowa ba. A da bankin platinum ne da shugaban bankin Patrick Atuche ke shugabanta.

DUBA WANNAN: Amurka zata janye daga Afghanistan, bayan sulhu da Taliban da ta yaka tun 2001

Babban bankin Najeriya karkashin a shugabancin Sanusi Lamido ya karbe bankin Platinum bayan da marigayi shugaba Umaru Yaradua yake shugabancin, inda ya amince da belin wasu bankuna saboda kudaden mutane da ke a bankunan.

Bankin Keystone ba kamfani bane kuma har yanzu mallakin gwamnatin tarayya ne karkashin jagorancin babban bankin Najeriya.

Babu wanda zai iya mallakar bankin da aka siyar dashi.

Atiku Abubakar dai ya tabbata mai nishadantarwa da bai kamata a dinga daukar maganganun shi da muhimmanci ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel