Bana sakaci kan harkar tsaro a Zamfara, inji gwamna Yari, wanda ke kasar waje

Bana sakaci kan harkar tsaro a Zamfara, inji gwamna Yari, wanda ke kasar waje

- Gwamna Yari ya dawo gida

- Ya zanta da manema labaru

- An caccake shi kan yawo kasashen waje

Bana sakaci kan harkar tsaro a Zamfara, inji gwamna Yari, wanda ke kasar waje
Bana sakaci kan harkar tsaro a Zamfara, inji gwamna Yari, wanda ke kasar waje
Asali: UGC

Dawowarsa ke da wuya Najeriya, gwamnan jihar Zamfara, AbdulAzizi Yari, ya maza ya zanta da manema labaru kan zargin da ake masa da ko-in-kula da ma sakaci kan aikinsa na tsaro a jiharsa, inda ana tsaka da makoki aka sami labarin baya ma jihar tasa.

Gwamnan, wanda ke ta katobarar siyasa a jihar tasa, kan 'yan takarkaru, ya saba da jin cece-kuce kan irin kalamansa, da ma sakacin da ake zargin gwamnatinsa kan tsaro, wanda a yanzu ake kwatantawa da yadda su Borno suke.

An dai saba kashe jama'a 20-30 jefi-jefi a jihar ta Zamfara a 'yan shekarun nan, kuma jami'an tsaro da aka tura, sun kasa hana mummunar ta'asar, duk da namijin kokari da suka ce suna yi.

DUBA WANNAN: An kammala kashi daya na jirgin kasan da zai taso daga Legas har zuwa Daura

Shugaba Buhari dai yayi Allah-wadai da kashe-kashen, kuma ya sake daukar mataki, sannan kuma ana sa rai shima gwamnan tunda ya dawo, zai zauna da manyan sarakunan sa da jami'an tsaro don gani yadda zasu shawo kan matsalar.

Jihar Zamfara na da talakawa da masu zama a karkara da yawa, tana kuma tafiya ne bisa tsarin shariar Islama, wadda aka sa rai zata hana ayyukan mugunta da zaluncin jama'a a tsakanin junansu, sai dai 'yan ta'addar, basu kula ba, jama'a kuwa, sun koma ga Allah.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel