Martanin uwargidan da aka wa caa kan ware mai aikinsu lokacin shaqatawa da Ice-Cream da Pizza a bidiyo

Martanin uwargidan da aka wa caa kan ware mai aikinsu lokacin shaqatawa da Ice-Cream da Pizza a bidiyo

- Lokutan shagulgula lokutan daina munanan halaye ne

- Amma ga wasu ba hakan bane

- Ba gwamnati bace kadai matsalar kasar nan ba, har da mutanen kasar

Lokacin shagali ne a don haka ne ake tunanin duk wasu munanan abubuwa kan yi kaura a cikin jama'a. Amma kuma an gano cewa ko a lakutan shakatawa da soyayya, kiyayya na tasiri. A hakan ne wani faifan bidiyo da ya bazu wanda ya nuna cewa lokutan shakatawa ba lokuta ne da ba a yin miyagun abubuwa ba.

Faifan bidiyon na nuna yanda ake tsangwamar wata karamar yarinyar. Yarinyar ta raka yan gidansu zuwa wani sanannen gurin cin abinci a Abule Egba, jihar Legas.

Ma'auratan sun saka kaya masu kala daya da yaran su. Daga gani kasan sunje gurin cin abincin ne don murnar lokacin a don haka ne suka ce a kawo musu kasaitattun ababen ci kamar su Pizza, ice cream, naman kaza da sauran su. Babu Bata lokaci suka fara cin abincin amma sukayi biris da karamar yarinyar.

DUBA WANNAN: Assha! Gasar inzali ta kai wani jarumin mata lahira, a zagaye na bakwai

Wannan yarinyar na sanye da bakar Riga ne zaune a wani teburin ,su kuma sauran suna dibar dadin su. Tana kallon su a yunwace amma basu san tana yi ba.

A faifan bidiyon ne matar da ta dauka take magana, tare da zargin yarinyar mai aiki ce. Tare da nuna bacin ranta akan yanda suka nuna mata halin ko in kula.

Matar na cewa "Wasu yan Najeriya basu da imani,ba gwamnati kadai ce matsalar mu ba, mutane ma matsala ne. Meyasa zasu yi haka a washegarin kirsimati? Kamar in ture teburin da suke cin abinci a kai"

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel