'An Kai wa 'Yan ADC Hari da Wukake da Sanduna a Hanyar Kamfen a Kebbi,' Amnesty
- Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai wa tawagogin kamfen ɗin jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi ranar 5 ga Nuwamba, 2026
- Ƙungiyar ta ce wasu ’yan daba ɗauke da makamai sun far wa motocin tawagogin, sun yi wa mutane duka da adduna, tare da lalata motocin da kayan aikin ’yan jarida
- Amnesty ta bayyana hare-haren a matsayin wani ɓangare na jerin farmakin da ake kai wa ’yan adawa a sassan Najeriya, tana mai buƙatar a yi bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Birnin Kebbi – Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai wa tawagogin kamfen ɗin jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta nazarci wasu bidiyoyi da ke nuna yadda wasu ’yan daba ɗauke da makamai suka far wa motocin tawagogin kamfen ɗin, tare da dukan mutane da adduna da kuma tare hanyoyi.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ta fitar a X, Amnesty ta ce hare-haren sun shafi ’yan jam’iyyar adawa, magoya bayansu da kuma ma’aikatan kafafen yaɗa labarai da ke bin tawagogin.
An far wa 'yan ADC a Argungu
Amnesty International ta ce wani bidiyo da aka ɗauka a Argungu ya nuna yadda wasu ’yan daba suka far wa mambobin jam’iyyar adawa, inda suka yi musu mugun duka tare da lalata motocinsu.
Ƙungiyar ta ce maharan sun yi amfani da wuƙaƙe da adduna wajen kai hare-hare, sannan suka riƙa jifan motocin da kwalabe da duwatsu.
Haka kuma, ta bayyana cewa maharan sun kai hari kan tawagar ’yan jarida da ke bin kamfen ɗin, inda suka lalata kyamarori da sauran kayan aikin da suke amfani da su wajen gudanar da aikinsu.
Korafin Amnesty kan hare-haren
Ƙungiyar ta bayyana cewa hare-haren na ƙara zama wata hanya ta danniya da ke hana ’yan adawa da magoya bayansu gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya
A cewarta, irin wannan yanayi na sa ya yi wuya ’yan Najeriya su yi amfani da haƙƙinsu na shiga ƙungiyoyi da gudanar da tarurrukan lumana.
Amnesty ta jaddada cewa bai kamata wani mutum ya rasa ransa ko fuskantar cin zarafi saboda shiga harkokin siyasa cikin lumana ba.

Source: Original
Ƙungiyar ta ce harin da aka kai wa ADC a Kebbi ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu hare-hare masu zubar da jini da aka kai wa kamfen ɗin jam’iyyar a Jihar Sakoto da ke maƙwabtaka da ita.
Ta bayyana cewa waɗannan abubuwa na daga cikin wani yanayi na hare-hare da ake kai wa ’yan adawa a sassa daban-daban na Najeriya.
Amnesty ta kuma zargi hukumomin Najeriya da gaza tabbatar da hukunta waɗanda suka aikata irin waɗannan laifuka a jihohi da suka haɗa da Neja, Kaduna, Edo da Enugu.
Kotu ta rusa takarar Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta rusa shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark.
Kotun ta soke matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa jam'iyyar ADC ta bayyana aniyarta ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin kotun a lokacin da ake kamfen.
Asali: Legit.ng
