Sanata Ben Bruce ya yabawa 'yansandan da suka tsere daga aiken da aka musu Sambisa

Sanata Ben Bruce ya yabawa 'yansandan da suka tsere daga aiken da aka musu Sambisa

- Sanata ya yaba wa 'yansada da suka tsere daga posting don kwas din na yaki da ta'addanci ne

- An sanya sunan su 200 don zuwa taya soji yaki

- Sanata Ben Bruce dan PDP ne, mai adawa da APC da Buhari

Sharuddan Saudiyya ga Najeriya kan hajjin 2019
Sharuddan Saudiyya ga Najeriya kan hajjin 2019
Asali: Depositphotos

Akalla 'yansanda 167 ne suka tsere daga kwas din da ake musu na atisayen yaki da ta'addanci, bayan da suka fahimci cewa in suka kammala kwas din yankunan da ake yaki da Boko Haram za'a shilla su domin taimakawa sojoji.

Sai dai duk da sauran 'yan Najeriya na Allah-wadai da karayar da mazan suka nuna, su kuma 'yan PDP, Sanata Ben Bruce da ma Reno Omokri, wadanda shaqiqan Goodluck Jonathan ne a wancan mulki, yabawa 'yansandan sukayi da wannan aika-aika.

Sanata Bruce, ya ce tunda aka yi harin Metele, aka kashe sojoji da dama, kuma shugaban kasa da mataimakinsa, da ma manyan soji basu je jana'iza ba, to lallai dole wadannan sojoji su kuka da kansu muddin aka aika su yakin da ake a arewa maso gabas.

DUBA WANNAN: An sake kai hari a ofishin kamfe na APC a kudu, an kona musu motoci

Ya kuma kara da cewa, sakacin da gwamnatin APC keyi kan yaki da ta'addanci yasa ake asarar mazan fama a yankunan da yanzu Boko Haram din ke barazana, take kuma dauki dai-dai kan mayakan.

A kwanan nan dai an kara wa 'yansanda albashi, kuma an kara yaye wasu, an kuma sake bude damar wasu su sake neman shiga aikin.

IGP Idris Kpotun dai, ya zabi 3,000 daga zaratan 'yansandan kasar nan don a koya musu yaki da ta'addanci, sannan a aika su yankin arewa mai nisa inda ake sa rai zasu fafata da Boko Haram ko a filin daga ko a lokutan zaben badi

Martanin 'yansanda na baya-bayannan dai yama zo ya karyata wannan batu, yace mutum 2,000 aka aika taya sojoji aiki a yankin arewa maso gabas, kuma suna can suna aikinsu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel