Kudin Faris Kulob: EFCC zata gurfanar da wasu gwamnoni

Kudin Faris Kulob: EFCC zata gurfanar da wasu gwamnoni

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) na duba yiwuwar bincikar wasu gwamnoni saboda karkatar da kudaden Faris Kulob ta hanyar amfani da wasu kamfanoni da suka taimaka masu wajen samun kudaden.

Wasu jihohi sun rasa sukunin samun kaso na karshe na kudaden Faris Kulob fiye da Dalar Amurka biliyan $2bn ba tare da amfani da wasu kamfanoni na musamman ba.

Kamfanonin sun bukaci karbar $350m kafin su tabbatar an saki kudaden zuwa ga jihohin.

Wani bincike ya gano cewar a yayin da kungiyar gwamnoni (NGF) ta amince da biyan kamfanonin kaso 2% na kudaden da zasu taimaka a karba, a gefe daya kuma yawancin jihohin sun yi alkawarin biyan kamfanonin kaso 5% zuwa 10%.

Kungiyar gwamnoni (NGF) tayi hayar kamfanonin Biz Plus da GSL domin taimakon jihohin wajen samun kasonsu na kudaden.

Sai dai wasu gwamnonin da basu dauki hayar kowanne kamfani ba sun biya kansu kaso 5% ko 10% na kudaden.

Kudin Faris Kulob: EFCC zata gurfanar da wasu gwamnoni

wasu gwamnonin jihohin Najeriya
Source: Depositphotos

Shugaba Buhari ya amince da biyan jihohi biliyan N522.74 a matsayin kaso na farko na kudaden.

Kowacce jiha ta karbi biliyan N14.5bn ko kaso 25%.

An sake sakarwa jihohin biliyan N243.79 a zagaye na biyu na rabon kudin Faris Kulob a watan Disamba na shekarar 2017.

Yayin rabon wannan kudaden ne aka gano cewar an biya kimanin biliyan N19bn ga kamfanoni a matsayin kudin tuntuba da kuma biyan dalar Amurka $86 zuwa asusun kungiyar gwamnoni.

DUBA WANNAN: Kisan mutane uku: Dan majalisar wakilai daga Kano ya shiga tsaka mai wuya

Tsawon shekaru biyu kenan hukumar EFCC na binciken biyan wadannan kudade na tuntuba.

An gano cewar an biya kimanin Dalar Amurka $183,000 zuwa wani kamfanin gwalagwalai da Sanatocin Najeriya da yawa ke da mu'amalar kasuwanci da shi.

Binciken EFCC ya gano cewar tsofi da gwamnoni masu ci da dama na da hannu a cikin karkatar da kudaden.

Majiyar EFCC ta tabbatar da cewar gwamnoni da yawa sun yanki kudaden tuntuba ba tare da daukar hayar wani kamfani ba, lamarin da yasa EFCC kulla damarar bincikar su da gurfanar wa, musamman ga wadanda suka bar gwamnati da kuma wadanda zasu bar mulki a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel