Allah ma ba zai bari a kwace mulki daga hannun APC a 2019 ba - inji wani babban Sarki

Allah ma ba zai bari a kwace mulki daga hannun APC a 2019 ba - inji wani babban Sarki

- Ubangiji ba zai bar wata jam'iyyar da ba APC ba cin zaben jihar Legas ba

- An kaddamar da sabon masallaci a harabar majalisar jihar Legas

- An hori masu amfani da masallacin dasu yi abinda ya dace na bauta

Allah ma ba zai bari a kwace mulki daga hannun APC a 2019 ba - inji wani babban Sarki
Allah ma ba zai bari a kwace mulki daga hannun APC a 2019 ba - inji wani babban Sarki
Asali: UGC

Oba din Legas, Oba Akiolu na daya yace Ubangiji ba zai bar wata jam'iyyar da ba APC ba cin zaben jihar Legas.

Oba Akiolu ya fadi hakan ne a jawabin shi na ranar asabar a karantarwar Hijrah ta duk shekara da bikin Bude sabon masallacin majalisa a majalisar jihar.

Yace sabon masallacin na da bambanci saboda ginin shi a cikin harabar majalisa inda ake kafa dokoki yake.

Shugaban ya shawarci masu amfani da masallacin da kada suyi abinda zai zubar da mutuncin addini.

Kakakin majalisar, Hon Mudashiru Obasa yayi jinjina ga mabiyan akan sadakar kudin da suka bada don kara gida masallacin.

Ya Kwatanta masallacin da gurin bautar Allah da tuna shi, kara da cewa masu amfani da masallacin su dage wajen bauta domin saboda hakan aka gida shi.

DUBA WANNAN: Assha! Gasar inzali ta kai wani jarumin mata lahira, a zagaye na bakwai

Babban bako na musamman a gurin shine gwamna Akinwumi Ambode wanda kwamishinan harkokin cikin gida, Dr. AbdulHakeem Abdulateef ya wakilta wanda shine babban limamin masallacin majalisar.

Shugaban taron kuwa shine Oba na jihar Legas kuma shugaban kungiyar sarakan jihar Legas, mai martaba Alaiyeluwa Oba Rilwan Osuolale Akiolu na daya.

A jawabin shi, shugaban musulman majalisar, Hon. Sikiru Osinowo yayi godiya ga Ubangiji da ya bada damar karasa ginin masallacin.

"Muna fara ginin masallacin don cike dalilin da yasa muke nan. Mu musulmai ne kuma Ubangiji ne ya bamu damar ginin sabon masallaci a lokacin Kakakin majalisa Rt. Hon. Mudashiru Obasa, " inji shi.

Malaman d sukayi jawabi a gurin sune, Abdullahi Hassan Inuwa da Shaykh AbdurRasheed Mayaleke.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel