Yawan marasa aikin yi qaruwa yayi daga bara zuwa yanzu a sabuwar kididdigar NBS

Yawan marasa aikin yi qaruwa yayi daga bara zuwa yanzu a sabuwar kididdigar NBS

- Yawan marasa aikin yi a Najeriya kullum karuwa yake

- Ya tashi daga mutane miliyan 17.6 zuwa miliyan 20.9

- Rahoton na nuna mutane masu karfi a jika (shekaru 15 zuwa 64) sun karu daga miliyan 111.1 zuwa miliyan 115.5

Yawan marasa aikin yi qaruwa yayi daga bara zuwa yanzu a sabuwar kididdigar NBS

Yawan marasa aikin yi qaruwa yayi daga bara zuwa yanzu a sabuwar kididdigar NBS
Source: Getty Images

Masu aikin yi sun karu daga miliyan 68.4 zuwa miliyan 68.72 daga 3 bisa hudu na 2015 zuwa uku bisa hudun 2016

Kididdigar NBS ta nuna cewa yawan yan Najeriya marasa aikin yin sun karu daga miliyan 17.6 zuwa miliyan 20.9.

Rahoton da suka saki a ranar laraba ya kunshi Kididdigar masu aikin yi daga karshen 2017 zuwa uku bisa hudun shekarar 2018.

Kamar yanda rahoton ya nuna, masu jini a jika wadanda zasu iya aikin daga shekaru 15 zuwa 64 sun karu daga miliyan 111.1 zuwa miliyan 115.5.

"Jimillar mutanen dake da aikin yi sun karu daga miliyan 68.4 a uku bisa hudun 2015 zuwa miliyan 68.72 a uku bisa hudun 2016, zuwa miliyan 69.09 a uku bisa hudun 2017 da miliyan 69.54 a uku bisa hudun 2018," inji rahoton.

"Jimillar mutanen da ke da aikin yi ( a kalla sa'a 40 a sati) sun karu daga miliyan 51.1 a uku bisa hudun 2017 zuwa miliyan 51.3 a uku bisa hudun 2018.

"Jimillar marasa aikin yi ko masu kananan abin yi ya ragu daga miliyan 13.20 a uku bisa hudun 2015 zuwa miliyan 11.19 a uku bisa hudun 2016 amma sai ya karu zuwa miliyan 18.02 a uku bisa hudun 2017 da kuma miliyan 18.21 a uku bisa hudun 2018.

DUBA WANNAN: Baqar yunwa da yara ke fama da ita a jihohin da ake yaki na hana su fahimtar karatu a makaranta - rahoton masana

"Jimillar mutanen da suke sahun marasa aikin yi kwata kwata ko suna aikin kasa da sa'a 20 a sati sun karu daga miliyan 17.6 a karshen shekarar 2017 zuwa miliyan 20.9 a uku bisa hudun 2018."

A cikin mutane miliyan 20.9 da basu da aikin yi, rahoton ya nuna cewa miliyan 8.77 a cikin su yanzu ne suka fara neman aikin yi, miliyan 0.93 basu da aikin yi ne sakamakon rasa aikin su da sukayi, sai kuma mutane miliyan 11.1 na aiki kasa da sa'o'i 20 a sati.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel