Wasu shu'uman mata 2 da ke garkuwa da mutane a Kaduna sun shiga hannu

Wasu shu'uman mata 2 da ke garkuwa da mutane a Kaduna sun shiga hannu

Hukumar 'yan sandan jihar Kaduna tayi nasarar damke wasu bata gari 12 ciki har da wasu mata biyu masu garkuwa da mutane Hashiya Dauda da Safara'u Mohammed Tahir masu shekaru 23 a duniya.

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce ta kama wasu gawurattatun mata masu garkuwa da mutane da wasu mutane 12 da ake zargin su da tayar da zaune tsaya a jihar Kaduna.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan 'yan sanda, Abdurrahman Ahmed ne ya bayar da wannan sanarwar a taron manema labarai da ya kira.

Wasu shu'uman mata 2 da ke garkuwa da mutane a Kaduna sun shiga hannu

Wasu shu'uman mata 2 da ke garkuwa da mutane a Kaduna sun shiga hannu
Source: Depositphotos

Mr Ahmed ya ce an kama uku daga cikin wadanda ake zargin ne saboda hadin baki wurin aikata laifi, garkuwa da mutane, mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba, yayin da wasu uku kuma an kama su ne saboda kisa, sata da kuma karbar kayan sata.

DUBA WANNAN: Barazana ga demokradiyya: Ku sa ido a kan Shehu Sani, Danjuma ya gargadi hukumomin tsaro

Wasu kuma ana zarginsa ne da aikata fashi da makami sai biyar daga cikinsu kuma an same su ne dauke da ganyen wiwi.

Ya ce mata biyun da ake zargi da garkuwa da mutane sune Hashiya Dauda da Safara'u Mohammed Tahir dukkansu masu shekaru 23 a duniya.

Sauran wadanda aka kama sun hada da Ishaq Sulaiman , Sale Ya’u, Yusuf Sulaiman da Iliyasu Ali.

"Wadanda ake zargi da fashi da makami sune Mark Pwa’ashino, Abdulganiyu Musa da Sabi’u Yusuf.

"Kazalika, wadanda ake zargi da dillancin miyagun kwayoyi sune Abdulkarim 25, Abdulsalam Yahaya a.k.a Danliti, Abdulsamad Yusuf, Solomon Bakari da Nura Ahmadu.

Ya bayyana cewa an same su da bindigu guda biyu, motocci guda biyar da ma wasu abubuwan. Ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel