Fadar shugaban kasa ta zargi Jonathan da jawowa Buhari tsaiko a nadin mukamai

Fadar shugaban kasa ta zargi Jonathan da jawowa Buhari tsaiko a nadin mukamai

Fadar shugaban kasa ta ce tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne dalilin da yasa shugaba Muhammadu Buhari ya samu jinkiri wajen nada ministocinsa.

An rantsar da Buhari ne a ranar 29 ga watan Mayun 2015 amma ya zabi 'yan fadarsa watanni shida baya a ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar ta 2015.

A hirar da akayi dashi a Channels Television a ranar Litinin, Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya ce Jonathan bai baiwa Buhari takardun mika mulki ba sai kwanaki 2 kafin ya sauka daga mulki.

Fadar shugaban kasa ta zargi Jonathan da jawowa Buhari tsaiko a nadin mukamai
Fadar shugaban kasa ta zargi Jonathan da jawowa Buhari tsaiko a nadin mukamai
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Ya ce, "Ikirarin da akeyi cewa Buhari ya kwashe kwanaki 166 yana zaban 'yan fadansa ba gaskiya bane. Zabar ministocin ya dauki lokaci ne saboda Jonathan bai bayar da hadin kai ga kwamitin sauya mulki ba.

"An bawa shugaban kasa takardun mika mulki sa'o'i 48 kafin rantsar da shi, shugaban kasar a wannan lokacin ya yanke hukuncin cewa babu yadda za ayi a samu gwamnatoci biyu a lokaci guda."

Sai dai mai maganawa da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku, Mr. Phrank Shuaibu ya ce Buhari ya saba jinginawa wasu mutane laifi a duk lokacin da abu ya faru.

Ya ce abin dariya ne jinkirin da Buhari ya yi wajan zaban Ministocinsa duba da cewa ya kwashe shekaru 12 yana takarar shugabancin kasa amma ya kashe sama da kwanaki 160 kafin ya zabi ministoci.

Ya kara da cewa, "Cewa shugaban kasa yana jiran takardun mika mulki kafin ya zabi ministocinsa alama ce da ke nuna bai shirya ya mulki Najeriya ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel