Kuma dai: EFCC ta saki hoton kasurgumin dan 419 ma'aikacin banki

Kuma dai: EFCC ta saki hoton kasurgumin dan 419 ma'aikacin banki

- Hukumar yaki da rashawa ta kama wani Dan damfara ma'aikacin banki

- Ya hada kai ne da wani inda suka damfari wata yar Hong Kong

- Ma'aikacin bankin ya bada bayanin, nan ba da dadewa ba za'a mika su gaban kuliya

Kuma dai: EFCC ta saki hoton kasurgumin dan 419 ma'aikacin banki

Kuma dai: EFCC ta saki hoton kasurgumin dan 419 ma'aikacin banki
Source: Facebook

Hukumar yaki da rashawa ta kama wani ma'aikacin banki da ya damfari wata yar Hong Kong har pam 79,000.

Ma'aikacin bankin kuma akawu na bankin Access, Ojo Adefemi Adedoyin, ana zargin su da wani Favour Oriafoh mai shekaru 30 da damfarar wata yar Hong Kong, Xu Yue har pam 79,000.

Hukumar yaki da rashawa ofishin yankin Uyo ne suka kama su.

Kamen nasu ya biyo bayan binciken karar da hukumar yan sandan Hong Kong ta mika na cewa an damfari budurwar wanda suka gano cewa a Najeriya ne.

Oriafoh da ya amsa laifin shi, ya bayyana sunan shi na damfarar Terry Mac ne ya bude shafin Facebook dashi don kawai ya damfari wanda ya fada tarkon shi.

"Ta fada sona a matsayi na na jami'in kwallon kafa mai suna Terry Mac, " inji shi.

Da soyayyar da take mishi yayi amfani har ya damfare ta kudin inda yayi amfani da daskararren asusun bankin wani Adeyemi Hassan Adedeji.

DUBA WANNAN: Sabon garambawul da za'a yiwa matatun man kasar nan bayan tazarce

A gurin binciken ne ya bayyana cewa wani ma'aikacin banki Adedoyin ne ya bashi daskararren asusun bankin da yayi amfani dashi.

"Yarjejeniyar ita ce ko nawa aka samu, da ma'aikacin bankin da mai asusun bankin zasu karbi kaso 15 cikin dari" ya bayyana.

Ma'aikacin bankin ya bada bayanai masu amfani ga hukumar kuma nan ba da dadewa ba za'a mika su kotu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel