Dan takarar gwamnan PDP a Legas yace Bola Tinubu ake kaiwa dukiyar jihar

Dan takarar gwamnan PDP a Legas yace Bola Tinubu ake kaiwa dukiyar jihar

- Agbaje ya kalubalanci Gwamnatin jihar Legas da ta tabbatar da yancin yada labarai

- Dan takarar yace da gangan ake boye shige da ficen kudaden jihar don ubangidan gwamnan ya samu hanyar shi

- Akwai bukatar a yanta jihar Legas daga kangin bauta, inji Agbaje

Dan takarar gwamnan PDP a Legas yace Bola Tinubu ake kaiwa dukiyar jihar
Dan takarar gwamnan PDP a Legas yace Bola Tinubu ake kaiwa dukiyar jihar
Asali: Depositphotos

Dan takarar gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP, Mista Jimi Agbaje, ya kalubalanci Gwamnatin jihar Legas karkashin mulkin jam'iyyar APC da ta tabbatar da yancin yada labarai wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yasa hannu a 2011.

Agbaje ya rubuta hakan ne a shafin shi na Facebook.

Dan takarar PDP ya musa cewa da gangan aka rufe shige da ficen kudaden jihar don a bawa ubangida hanyar shi ta samu.

Yace akwai bukatar a yanta jihar Legas daga kangin bauta da take ciki.

Agbaje yace, "Jam'iyyar mai mulki ta zarge mu da yankin neman zabe ba ta sigar da ta dace ba saboda mun kalubalanci mulkin ta ta bangaren boye boyen Gwamnatin ta fannin kudi."

"Kin tabbatar da yancin yada labarai na jihar Legas ya bar mutanen jihar a duhu na tsawon lokaci akan yanda al'amuran jihar ke gudana. Al'amura na faruwa amma an boye mana. "

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APGA na magagin wargajewa gabanin 2019

" Yan jihar Legas nason Gwamnatin da zata maida bukatunsu kan gaba fiye da umarnin mutum daya - gidaje, cibiyoyin kiwon lafiya, aiyuka, damammaki ga matasa da sauran su. Nasan hakan ne saboda naji hakan daga ko'ina. Mutane sun gaji da rufa rufa. Karamin abu ne Yan jihar su kawo sabon tsari a jihar Legas a zabe mai zuwa. Garesu a yanzu, Legas bata da yanci. "

Dan takarar jam'iyyar PDP din yana mamakin yanda APC a jihar Legas zata iya ma mutane alkawarin rayuwa mai inganci bayan tireloli da motocin daukar kaya na nan a jere a gefen tituna wanda hakan ke kawo cunkoso da wahalhalu ga masu ababen hawa.

Yace ta hanyar tsawwala haraji ne APC tasa kudin mota a cikin jihar yayi tsada tare da sa ma rayuwar mutanen jihar wahalar da basuyi tsammani ba. "

Agbaje ya kara da cewa, " Burin mu na samar wa jihar Legas yanci ba wai a baki bane kawai, da gaske muke kuma mun fara da mata da maza a fadin jihar wadanda suka yarda Legas zata fita daga kangin da take ciki. "

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel